Daily Trust Aminiya - BIDIYO: ‘Musulmi ba su yi asara ba don sun yi ibada a gida’
Subscribe
Dailytrust TV

BIDIYO: ‘Musulmi ba su yi asara ba don sun yi ibada a gida’

A daidai lokacin da azumin Ramadan ke ban-kwana, malamai da masana na kara azama wajen nusar da al’ummar Musulmi hanyoyin ribatar watan duk da halin da duniya ke ciki.

A wasu wuraren dai an kafa dokar hana tarukan addini, lamarin da ya sa babu damar yin sallah cikin jama’a a yunkurin hana yaduwar coronavirus.

Shaikh Ibrahim Sulaiman na cikin malaman da ke ganin ko a gida Musulmi suka yi ibada a kwanaki goma na karshen watan Ramadan to kamar sun yi a masallaci ne.