Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Bidiyon tsiraici: Ba ni na dauki Maryam Booth ba, inji tsohon saurayinta

Bidiyon tsiraici: Ba ni na dauki Maryam Booth ba, inji tsohon saurayinta

Tsohon saurayin fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Booth, Ibrahim Ahmad Rufai wanda aka fi sani da Deezell ya karyata batun cewa shi ne ya dauki bidiyon Maryam Booth tsirara, kuma yada shi.

Deezell ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tiwita wanda aka tabbatar @officialdeezell, inda ya tabbatar da cewa ya taba yin soyayya da jarumar, amma kuma bai san wanda ya dauki wannan bidiyon da ake yadawa ba, ballantana ma ya rika amfani da shi wajen neman kudi a wajenta.

“Ban taba nadar faifan bidiyon ta a boye ba lokacin da take canja kaya ba. Haka kuma ban san wanda ya dauke ta bidiyon ba.”

Haka kuma a martanin nasa, Deezell ya bukaci Maryam Booth ta nemi gafararsa ta hanyar janye maganar da ta yi, wanda a cewarsa za ta bata masa suna.

Idan ba a manta ba, a makon jiya aka rika yada wani bidiyo wata budurwa tsirara, inda aka rika cewa Maryam Booth din ce.

Faifan bidiyon ya jawo cece-kuce, inda wasu suke cewa ita cewa ita ce, suna Allah wadai, wasu kuma suka rika ba ta kariya, tare da cewa ba halinta ba ne.

Ana cikin haka ne, a ranar Asabar da ta gabata Maryam Booth ta fitar da sanarwa cewa wani tsohon saurayinta mai suna Ibrahim Ahmad Rufai ne ya saki bidiyon.

A bayanin da ta wallafa a shafinta na Instagram, Maryam ta ce tsohon saurayin nata mai suna  Ibrahim Ahmad Rufai wanda ake kira Deezell ne take zargi da sakin bidiyon.

Kuma ta kara da cewa za ta dauki matakin hukuma.

Shi ne kuma shi ma wanda take zargin ya fito da tasa sanarwar, inda shi ma ya bukaci ta janye batun domin kada ta bata masa suna.

 

 

Martanin Maryam Booth
Martanin Deezell