Da Dumi Dumi

Bikin Kirisimeti: ’Yan kasuwa sun koka kan karancin ciniki

A daidai lokacin da ake ci gaba da shagulgulan bikin Kirisimeti kuma ake shirye shiryen shiga sabuwar shekarar 2020 wadansu ’yan kasuwa a Legas sun koka kan karancin ciniki lamarin da suka danganta da karancin kudi a hannun jama’a.

Aminiya ta zagaya wasu kasuwannin  Legas don ganin yadda hada-hadar ciniki ke tafiya a wannan lokaci. Malam Ibrahim Mu’azzam dan kasuwa ne da ke sayar da kayan gwari da suka hadar da tumatir da attarugu ya shaida wa Aminiya cewa, suna taba kasuwa gwargwadon hali.

“Muna taba cinikin daidai wa daida babu abin da za mu ce sai godiya. A daidai wannan lokaci an sauke mana manyan motoci kuma duk sun kare ka ga yadda wajen namu yake a yanzu babu kayan, farashin tumatir ya danganta domin hawa-hawa ne akwai wanda ake sayarwa kwando Naira dubu 7 akwai na dubu 8 akwai na dubu 5 har da na 3500 ana samu,” inji shi.

Ya ce ana samun attarugu kananan buhu a kan Naira dubu 5 zuwa dubu 6, manyan buhuna kamar buhun fulawa ana samu a kan Naira dubu 13 zuwa 14 sai wanda ya fi haka a kan Naira dubu 15 zuwa 16. Ya ce an samu karuwar farashi lura da bukukuwan Kirsimeti da gabatowar sabuwar shekara saboda karuwar bukatar kayayyakin a wannan lokaci. Ya ce saukin abin shi ne kayayyakin sun samu daga Arewa, wadatar kayayyakin ne ya sanya abin ya zo da sauki.

ADVERTISEMENT

Ita ko Bukula Ariyo da ke sayar da sinadaran girki a Kasuwar Ilepo, kayayyakin da suka hada da nau’o’in magi da kori da man salad da makamantansu, ta shaida wa Aminiya cewa, “Babu ciniki idan an kwatanta da shekarun baya. Ta ce rufe iyaka da aka yi ya sanya farashin kayayyakin da suke sayarwa sun tashi. “Ana danganta hauhawar farashin kayayyakin namu da rufe iyaka, yanzu haka muna lokacin kakar cinikin na Kirsimeti da sabuwar shekara amma saboda tsadar kayayyakin da rashin kudi a hannun jama’a daidaiku ne ke zuwa suna sayen kadan kadan,” inji ta.

Malam Muhammad Warshu Adam, dan kasuwa ne da ke sauke albasa a Kasuwar Ilepo, cewa ya yi, kasuwanci babu abin da za su ce sai dai su yi wa Allah godiya. Ya ce ana taba kasuwa kamar yadda ya kamata sai dai ba a rasa kalubale da suke fuskanta a kasuwar. Ya ce a bangarensa hada-hadar kasuwancin na bana ta fi ta bara, saboda a bara yana sauke mota daya ce zuwa biyu na albasa.

“Amma yanzu daga jiya zuwa yau an sauke mota ta kai 4 kuma wadansu ma na tafe kuma Allah cikin ikonSa ga shi kayan da aka sauke ya kare saura kadan. Ka ga alamu ne na ana ciniki, albasa iri biyu ce akwai wacce ake sayarwa buhu Naira dubu 30 akwai ta Naira dubu 36 sannan akwai ta Naira dubu 26, sai kuma tsohuwa har yanzu tana kaiwa Naira dubu 40,” inji shi.

Ya ce kadan daga cikin kalubalen da suke fuskanta shi ne lalacewar hanyoyi a Arewa. “A yanzu idan direba ya dauko kaya daga Kwantagora zuwa Makera, hanya ce wacce tafiyarta ba ta wuce awa biyu amma saboda lalacewarta sai direba ya kwashe awa 11 zuwa 12 yana fama a wajen, yanzu haka ina da direban da bai iso ba, lalacewar hanya da barayin mutane sun tare hanyar direban da yaran Allah Ya tsallakar da su, fatarmu gwamnati ta gyara hanyar,” inji shi.

Shi ma Muhammadu Nda da ke sayar da citta da karas da kabeji da tafarnuwa da makamantansu ya ce a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekarar suna taba ciniki sosai sai dai matsalar da suke fuskanta ita ce kayayyanki irin su citta na neman yankewa a kasuwa saboda ba sa samun manyan motoci daga Arewa da za su yi musu dakon kayan.

“Babbar matsalarmu ke nan babu mota a can Arewa, saboda masu bukatar kaya kowane iri a wannan lokaci sun yi yawa, sannan abokan cinikinmu na kokawa kan tsadar kayayyakin masarufi a Kirsimeti da sabuwar shekara, sannan muna fama da matsalar lalacewar hanya, inda mota ta dauko maka kaya sai ta yi kwana 4 zuwa 5 a hanya, kafin ta iso kayan sun fara lalacewa don haka muna so gwamnati ta tausaya mana,” in i shi.

Aminiya ta zanta da wadansu da suka shigo kasuwar domin sayayyar bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara. Madam Susan ta shaida wa Aminiya cewa, ta je kasuwar ce domin ta yi siyayyar bukukuwan. Ta ce kayayyakin sun yi dan karen tsada ga shi babu kudi a hannun jama’a, “Har yanzu babu ci gaba na a-zo-a-gani a fannin tattalin arziki,” inji ta.

Da yawa daga cikin ’yan kasuwar da masu saye sun nuna godiyarsu ga Allah da Ya kawo su wannan lokacin cikin koshin lafiya.

Share