Da Dumi Dumi

Bikin kirkiro Jihar Jigawa sharholiya ce – Habibu Sara

Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa
Gwamna Badaru Abubakar na Jihar Jigawa

Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar Jigawa Alhaji Habibu Sara ya ce bikin da ake yi don murnar kirkiro jihar sharholiya ce, don haka ne ya sa ba za su yi ba. Alhaji Habibu Sara ya shaida wa Aminiya cewa: “Mu gwanatinmu ta APC ba gwamnatin ’yan sharholiya ba ce shi ya sa ba za mu yi bikin cikar shekara 28 da kirkiro jihar ba, domin Gwamnatin APC gwamnati ce ta tsantseni da taimaka wa wadanda suke cikin damuwa.”

Alhaji Habibu Sara ya ce maimakon su debi kudin gwamnati a yi sharholiya da facaka gara su kashe kudin wajen taimaka wa wadanda suka gamu da bala’in ambaliyar ruwan sama da rugujewar muhalli, sabanin yadda gwamnatin baya ta yi.

Alhaji Sara ya kara da cewa irin wannan taro ba ya da wata fa’ida a wajen mutanen Jigawa domin su mutanen  ba taro suke bukata ba, abin da suke bukata a kare musu dukiyarsu kuma a yi musu ayyuka da ita, ta wajan gina hanyoyi da samar da ruwan sha da sauran ayyukan raya kasa.

Da yake mayar da martani Alhaji Salisu Mamuda na Jam’iyyar PDP cewa ya yi maganar tsantseni da Habibu Sara ke fadar suna yi babu ita, domin gwamnati ce da ba ta damu da talakawa ba,  kullum Gwamna ba ya gari, kuma in ban da ayyukan da tsohuwar gwamnati ta fara babu wani aiki da za suyi tinkaho cewa gwamnatin APC ta yi.

ADVERTISEMENT
Share