✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata (2)

A yau muna dauke ne da amsoshin tambayoyi biyu da daya daga cikin shahararrun masu karatu ya rubuto.  Ta farko a shekarar 2009 ya aiko,…

A yau muna dauke ne da amsoshin tambayoyi biyu da daya daga cikin shahararrun masu karatu ya rubuto.  Ta farko a shekarar 2009 ya aiko, inda a ciki yake son sanin tsarin zazzabin wata.  A dayan kuma, wanda ya rubuto a cikin shekarar 2011, yana neman bayani ne kan ko zai yiwu mutum ya iya takawa a kan wata sanadiyyar bulaguro don binciken ilimi.  Ga amsoshin da na ba shi nan kasa.  A sha karatu lafiya.

Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: me yake kawo rashin lafiyar wata (Moon Eclipse)?  Jama’a na cewa rana ce take kama shi.  Yaya abin yake ne Malam?

Aliyu Mukhtar Sa’idu, Kano: 08034332200

A hakikanin gaskiya Malam Bahaushe ne ke amfani da kalmar “zazzabi,” saboda irin yanayin da wata ke bayyana idan hakan ta faru, wato ya fito a gurgunce, babu haske; bayan watakila ya kai kwana 20 ko goma sha. Da farko dai, rana da wata kowannensu na tafiya ne a falakinsa, wato hanyar da Allah Ya tsara masa, a sararin samaniya. Bayan haka, kowanne daga cikinsu na da iya kwanakin da Allah Ya iyakance masa ne kafin ya gama gewaye daya. Wata kan kwashe kwana 29.5 kafin ya gewaye wannan duniya tamu. A yayin da rana ke daukar kwana 25 kafin ta gama gewaye guda daya a cikin tafarki ko falakinta.

Sannan, dukkan duniyoyin da ke makwabtaka da rana suna gewaye da ita ce, kuma kowanne daga cikinsu na da tauraronsa, wato Satellite ke nan a Turance. Tauraron wannan duniya tamu shi ne wata da ke gewaye ta a dukkan kwanakin nan 29.5, ko kwana 30 a takaice.

Wannan gewaye da wata ke yi wa wannan duniya tamu, yana yi ne a lokacin da halittar rana ita ma take nata gewayen. Kasancewar saurin tafiyarsu ba daya ba ne, wannan ya sa a daidai lokacin da rana ke juya mana baya, a lokacin kuma wata ke darsano hasken rana, don ya haskaka mana duhun da ke fuskantarmu yayin da muka shiga duhu.  Zai dace mai karatu ya san cewa wata ba ya da hasken kansa. A’a, hasken da ke samunmu daga wata hasken rana ne.  Wannan ya sa Allah Ya siffata wata da kalmar “Nuran”  a cikin Alkur’ani, wato wanda ke haskakawa, ba mai bayar da hasken ba.

Ita kuma rana aka siffata ta da kalmar “Sirajan,” wato fitila mai bayar da haske. Wannan hikima  ce ta Ubangiji; a yayin da rana ta kewayo mu kuma, sai haskenta ya bice na wata. Amma da zarar ta juya mana baya, takan darkake wata ne a lokacin da yake gewayensa ga wannan duniyar tamu; ma’ana lokacin da yake cikin falakinsa – sai ta haskaka shi, shi kuma nan take sai ya haskaka duniya, iya gwargwadon kwanakinsa.

To a wasu lokuta akan samu akasi; maimakon idan rana ta juya mana baya har muka shiga duhu a ce wata ya hasko mana haskensa da ya samo daga hasken rana, sai ya zama a lokacin yana bayan wannan duniyar tamu, cikin duhun da rashin hasken ranar ya samar.  Tunda har yana cikin duhu ne, babu yadda za a yi mu ga haskensa.  Sai ya zama ja, babu haske. A wasu lokuta ma sai dai a ga hanakinsa kawai, amma ko gudan watan ba a gani. Hakan ke nuna cewa wannan duniyar tamu ta shiga tsakanin rana da wata ke nan, kuma hakan, shi ake kira Lunar Eclipse a Turance.

Idan har ya zama lokacin da muka shiga duhu, wata na cikin inuwar da duniyar ta baro a bayanta ne (wato “Umbra,” inji Malaman Sararin Samaniya), kamar yadda bayani ya gabata, wannan shi ake kira Complete Lunar Eclipse.  Amma idan a lokacin da rana ta juya mana baya muka shiga duhu, wata bai gama shiga duhun da duniyar ta baro a baya ba, to za a samu haskensa kadan, amma kana ganinsa ka san akwai matsala. Wannan kuma shi ake kira Partial Lunar Eclipse. Wannan abin da ya shafi wata ke nan.

Amma idan kuma wata ne ya shiga tsakanin rana da wannan duniyar tamu, to za mu shiga duhu ne iya gwargwadon tsawon lokacin da watan zai dauka kafin ya fice daga farfajiyar hasken ranar da ya tare mana. Wannan kuma shi ake kira Solar Eclipse. Shi ne ke haddasa samuwar dusashewar hasken rana lokacin yini. Ba dukkan duniyar ba ce ke shiga duhu, a’a, daidai banganren duniyar da wata ya tare hasken ne ke shiga duhu. Wannan shi ne abin da ke faruwa, a kimiyyance, kuma alama ce da ke nuna sauyawar yanayin da duniya ke gudanuwa a kai. Wannan tasa a Musulunce Manzon Allah (SAW) ya umarce mu da mu rika yin Salla da sadaka da istigfari da hailala a duk lokacin da hakan ya faru. Domin alamar fushin Ubangiji ne. Kuma alama ce da ke tuna wa mutane yadda aukuwar Kiyama za ta kasance (wato daga bicewar hasken rana, zuwa rushewar duniya baki daya).

Amma babban dalilin da malaman kimiyya ba su hangowa, shi ne hakan na faruwa ne sanadiyyar sabo da bayi ke aikatawa a doron wannan kasa. An samu irin wannan yanayi lokacin Manzon Allah (SAW), daidai lokacin da dansa Ibrahim ya rasu, rana ta yi kusufi.  Nan take sai wadansu suka fara cewa ai don rasuwar dansa ne. Da ya ji haka, sai ya tashi ya rika bi kwararo-kwararon Madina, yana cewa: “Lallai rana da wata ayoyi ne guda biyu daga cikin ayoyin Allah; don haka ba su yin kusufi don mutuwar wani ko don rayuwarsa.”  A takaice dai, idan wannan duniyar ta shiga tsakanin hasken rana da wata, ta yadda wata ya zama yana cikin duhu, shi ke haddasa samuwar husufin wata, wato Lunar Eclipse.  Idan kuma wata ya shiga tsakanin hasken rana da wannan duniyar tamu, hakan na haddasa samuwar kusufin rana, wato Solar Eclipse.  Da fatan ka gamsu. (TAMBAYA, 2009)

Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce ko mutum zai iya tafiya a kan doron wata (Moon) domin wani bincike a kansa? Daga Aliyu Mukhtar Sa’idu (I.T) Kano, [email protected] 08034332200

Malam Aliyu ai tuni har an yi kuwa. Abu ne mai yiwuwa, kamar yadda tarihi ya nuna lokacin tafiyar su Neil Armstrong a 1969. Sun taka saman wata, inda suka gudanar da binciken da suke son yi. A karshe suka debo samfurin kasar wurin, don shigowa da shi duniya da ci gaba da gudanar da bincike kan yanayin wurin.  Sai dai kuma ya kamata mu sani, muhallin da ke saman wata ya sha bamban da irin muhallinmu.  Domin a yayin da muke da iska mai kadawa da muke shakarta a nan, a can babu irin wannan iska. Don haka masu zuwa duniyar wata ke sanya wasu tufafi masu dauke da na’urar shakar iska, wacce ke taimaka musu wajen numfasawa yadda ta kamata.  Sannan a can babu tsarin janyo nauyi kasa, wato “Force of Grabity” kamar yadda muke da shi a sararin wannan duniya tamu. Wannan ya sa za ka gansu kamar suna tafiya ne a saman iska, ba su daidaituwa wuri daya a lokaci daya, saboda karancin tasirin wannan tsari a can.  Da fatan ka gamsu.