Search
Subscribe
Bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata (3)

Bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata (3)

A wannan mako, cikin waiwaye adon tafiya kan ilimin sararin samaniya, sanadiyyar murnar cika shekara 50 da aka yi da fara zuwa duniyar wata, mun dauko tambayar da Nasiru Kainuwa Hadeja ne ya aiko a shekarar 2017, wadda a ciki yake son sanin yadda ake tafiya a duniyar wata.  A sha karatu lafiya:

Baban Sadik barka da wannan lokaci. Da gaske ne a duniyar wata da jan-kafa ake tafiya ba a daga kafa? Kuma da gaske ne cikin watan ake shiga idan aka je duniyar watan?  Nasiru Kainuwa Hadeja mail:nasirukainuwahadejia1@gmail.com

Malam Nasiru barka ka dai.  Da farko dai yana da kyau ka san cewa wannan duniya tamu ba ta da wani tauraro na asali (Natural Satellite) da ya wuce wata, kuma idan aka kwatanta shi da girman duniyar, kusan shi ne tauraron asali da ya fi girma a dukkan Taurarin Asali da ke gewaye da sauran duniyoyin da ke makwabtaka da mu.  Shi Wata ba ya da hasken da yake kyallarowa na kansa, sai dai ya lakato haske daga rana a yayin da take nata shawagin, idan ta juya mana baya kuma muka shiga dare ko duhu, sai ya hasko mana wannan haske.

Kamar wannan duniya tamu da sauran duniyoyi ko halittun da ke sama, Wata a cure yake, ko in ce a mulmule. Bangaren da ke fuskanto mu a lokacin da yake shawagi, shi ake kira “The Near Side,” a Turancin Kimiyyar Sararin Samaniya. Wannan bangare ne ke darsano hasken rana don haskaka duniyarmu. Kuma an kiyasta cewa darajar zafin da ke wannan bangare ya wuce digiri 137 a ma’aunin zafi na santigireti (wato 1370C).  Daya bangaren da ke shiga duhu kuma daga baya, shi ake kira “The Far Side.”  Amma kuma sabanin bangaren farko, wannan bangare bai da zafi sai sanyi mai tsanani. An kiyasta sanyin wannan bangare na Wata cewa ya kai 156 a kasa da mizanin zafi (wato -1560C).

Binciken baya-bayan nan da aka yi ya tabbatar da cewa halittar Wata na dauke ne da duwatsu nau’uka daban-daban, da sinadaran kimiyya masu inganci irin wadanda ba mu da su a wannan duniya tamu. Kari a kan haka, jikin Wata, inji masu wannan bincike, kamar gilashi yake wajen mu’amala da haske; duk ta inda ka cillo haske, zai dauka, ya kuma cilla hasken zuwa inda yake fuskanta.  Kamar dai yadda gilashi ke yi idan ka cilla masa haske.  Wannan ya sa idan rana ta cillo haskenta, sai Wata ya dauka, ya kuma cillo hasken zuwa wannan duniya tamu, kasancewar shi ne tauraronmu. Allah Buwayi Gagara Misali!

Ba nan aka tsaya ba, babu iska balle guguwa a duniyar Wata. Wannan ya sa duk inda ka taka a saman Wata, gurabun sawunka za su ci gaba da kasancewa a wurin, tsawon zamani. Har zuwa yau akwai gurabun takun wadanda suka ziyarci duniyar Wata tun 1969 a Kumbon Apollo 11.  A karshe, akwai baraguzan taurarin da rayuwarsu ta kare (wato Meteorite) masu shawagi a saman Sararin Samaniya, wadanda kuma ke shigowa wannan duniya tamu lokaci-lokaci. Ire-iren wadannan baraguzai ne ke afkawa cikin Wata a lokuta daban-daban, iya gwargwadon girmansu.  Don haka Malaman Kimiyyar Sararin Samaniya suka ce galibin ramuka da tsagar da ke jikin Wata sun samo asali ne sanadiyyar illolin da wadannan baraguzai masu shawagi a can sama ke yi a saman Wata.

Bayanan da suka gabata na tabbatar da cewa wannan muhalli da Wata yake, muhalli ne da yanayinsa da dabi’unsa suka sha bamban da wanda muka saba da shi a wannan duniya tamu. Don haka yanayin tafiya ya sha bamban da yadda muke tafiya a wannan duniya. Domin a wannan duniyar akwai iska dake kadawa iya gwargwadon yadda ta dace da rayuwarmu. Shi ya sa ma malaman kimiyya suka ce, bayan sun gudanar da bincike na kwakwaf kan ko za a iya samun wata duniya wacce dabi’u da yanayinta suke daidai da wannan duniyar tamu, amsar ita ce a’a.  Kuma wannan ke tabbatar maka da cikakkiyar hikimar Ubangiji da kudirarSa da gamewar iliminSa wajen halitta da tafiyar da ita. Inda Ya zaunar da mu a wannan duniya, wadda ita ce ta dace da mu, ta la’akari da rayuwarmu.  Yadda Bature ya kware wajen binciken kimiyya da fasahar kere-kere, ta la’akari da inkarin da yake wa samuwar Ubangiji, da a ce akwai wata duniyar da dan Adam zai iya rayuwa cikinta kamar yadda wannan duniyar take, komai da komai iri daya da tuni Bature ya fara tunanin komawa wata duniyar don sake gudanar da rayuwa.

Amsar tambayarka ta cewa ko idan suka je suna shiga cikin watan ne, a’a. Bayanan da suka gabata kadai sun isa su tabbatar maka cewa halittar Wata curarriyar halitta ce, ba wai kogo ba ne; babu koguna a jikin Wata, sai dai alamun baraguzan da ke fadowa cikinsa lokaci-lokaci daga sararin samaniya.

Wannan shi ne dan abin da ya samu na jawabi. Da fatan ka gamsu.

 

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin