Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata (4)

A wannan mako ga mu dauke da daya daga cikin bayanan da suka gabata kan ma’anar wata da tarihinsa da kuma yanayin rayuwarsa. Wannan bangare ne na makalar da muka gabatar a shekarar 2010 mai taken: “Tsaga a Jikin Wata: Mu’jiza ko Yawan Shekaru?” Wadannan bayanai na zuwa ne cikin bayanan da muke kwararowa kan bikin murnar cika shekara 50 da fara zuwa duniyar wata.  A sha karatu lafiya:

Halittar wata: Daga ina haka?

ADVERTISEMENT

Bayani kan daga ina Wata ya samo asali bai kamata ya dame mu ba, musamman ganin cewa a jerin kasidun da muka gabatar a shekarar da ta gabata, masu taken: “Kimiyyar Kur’ani da ta zamani: A ina aka hadu?,” mun yi wannan bayani.  Abin da ke da muhimmanci mu sani shi ne, shi Wata, ko Moon a Ingilishi, shi ne Tauraron Asali (Natural Satellite) da wannan duniya tamu ta mallaka, kuma yake gewaye ta, tare da halittar rana.  Malaman Sararin Samaniya sun yi hasashen cewa akalla halittar Wata ta yi shekara biliyan hudu ko sama da haka, tun samuwarta.  Wata kan kare gewaye wannan duniya tamu ne cikin kwanaki 25 da rabin kwana (25.5 days), amma idan aka hada da gibin kwanakin da yake kashewa a halin shawaginsa a falakin rana, sai ya yi kwanaki 29 da rabin kwana (29.5 days) yake gama gewaye daya.

Kamar yadda bayanai suka gabata a sama, wannan duniya tamu ba ta da wani Tauraro na Asali (Natural Satellite) da ya wuce Wata, kuma idan aka kwatanta shi da girman duniyar, kusan shi ne Tauraron Asali da ya fi girma a dukkan Taurarin Asali da ke gewaye da sauran duniyoyin da ke makwabtaka da mu.  Shi Wata ba ya da hasken da yake kyallarowa na kansa, sai dai ya lakato haske daga rana a yayin da take nata shawagin, idan ta juya mana baya kuma muka shiga dare ko duhu, sai ya hasko mana wannan haske, kamar dai yadda bayanai suka gabata a kasidun baya. Kamar wannan duniya tamu da sauran duniyoyi ko halittun da ke sama, Wata a cure yake, ko in ce a mulmule.  Bangaren da ke fuskanto mu a lokacin da yake shawagi, shi ake kira, The Near Side, a Turancin Kimiyyar Sararin Samaniya.  Wannan bangare ne ke darsano hasken rana don haskaka duniyarmu, kuma an kiyasta cewa darajar zafin da ke wannan bangare ya wuce digiri 137 a ma’aunin zafi na santigireti (wato 1370C). Daya bangaren da ke shiga duhu kuma daga baya, shi ake kira The Far Side. Amma kuma sabanin bangaren farko, wannan bangare bai da zafi sai sanyi mai tsanani.  An kiyasta sanyin wannan bangare na Wata cewa ya kai 156 a kasa da mizanin zafi (wato -1560C).

ADVERTISEMENT

Binciken baya-bayan nan da aka yi ya tabbatar da cewa halittar Wata na dauke ne da duwatsu nau’uka daban-daban, da sinadaran kimiyya masu inganci irin wadanda ba mu da su a wannan duniya tamu. Kari a kan haka, jikin Wata, inji masu wannan bincike, kamar gilashi yake wajen mu’amala da haske; duk ta inda ka cillo haske, zai dauka, ya kuma cilla hasken zuwa inda yake fuskanta.  Kamar dai yadda gilashi ke yi idan ka cilla masa haske. Wannan ya sa idan rana ta cillo haskenta, sai Wata ya dauka, ya kuma cillo hasken zuwa wannan duniya tamu, kasancewar shi ne tauraronmu. Allah Buwayi gagara misali! Ba nan aka tsaya ba, babu iska balle guguwa a duniyar Wata. Wannan ya sa duk inda ka taka a saman Wata, gurabun sawunka za su ci gaba da kasancewa a wurin, tsawon zamani. Har zuwa yau akwai gurabun takun wadanda suka ziyarci duniyar Wata tun 1969 a Kumbon Apollo 11.

A karshe, akwai bura-guzan taurarin da rayuwarsu ta kare (wato Meteorite) masu shawagi a saman Sararin Samaniya, wadanda kuma ke shigowa wannan duniya tamu lokaci-lokaci. Ire-iren wadannan bura-guzai ne ke aukawa cikin Wata a lokuta daban-daban, iya gwargwadon girmansu. Don haka Malaman Kimiyyar Sararin Samaniya suka ce galibin ramuka da tsagan da ke jikin Wata sun samo asali ne sanadiyyar illolin da wadannan bura-guzai masu shawagi a can sama ke yi a saman Wata.  Wannan shi ne dan abin da zai samu na bayani kan yanayin da Wata ke rayuwa a ciki.