Da Dumi Dumi

Binciken kwakwaf: Kurona ta samo asali ne daga China

Kurona ta samo asali ne daga China
  • Cutar na ci gaba da yaduwa a duniya

Ga dukkan alamu cutar Kurona wadda ta fara bayyana a karshen  watan Disamban bara a birnin Wuhan a Lardin Hubei na kasar China, tana neman sanya wa kasashen duniya takunkumi. Hukumomin lafiya na duniya sun yi kiyasin cewa fiye da mutum dubu 200 ne suka kamu da cutar a sassan duniya yayin da ta yi ajalin kimanin 8000 daga cikinsu. A ranar 11 ga watan Maris Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta shelanta cutar da  ‘annoba ta duniya’  yayin da ta shafi fiye da kasashe 150 a yanzu.

China ce ta fi samun adadin mutanen da suka harbu da cutar; yayin da Italiya ke rufa mata baya, kuma a ’yan kwanakin nan kasashe da dama na ta  daukar matakan kariya ko yakar cutar da aka sanya wa Cobid-19.

Bincike kwakwafi: Kurona ta samo asali daga China – Nazarin Masana

A wata makala da Cibiyar Nazari kan Dunkulewar Duniya ta wallafa kuma ta yadu a kafofin sadarwar zamani ta nuna cewa wai cutar ta samo asali ne daga wajen China.

Labarin da aka wallafa ranar 11 ga Maris yana kafa hujja ce da wani labarin da shi ma aka wallafa a shafin daga mutum guda mako guda kafin na biyun, inda ya ce “Mai yiwuwa cutar ta samo asali ne daga Amurka.” Labarin mai taken “Wani sabon bayani mai sa kaduwa. Ko shin cutar ta samo asali daga Amurka?” Rubutun farkon da aka wallafa  ya yi ikirari mai yawa kan cutar da za a dora ayar tambaya a kai, sa’annan ya ci karo da abin da nazari da rahotannin kafofin labarai suka tabbatar.

ADVERTISEMENT

Jigon sakon labaran biyu da aka yi ranakun 4 da 11 ga Maris – mai yiwuwa COBID-19  sojojin Amurka ne suka shigo da cutar zuwa China -ya ce a kwanakin baya ne wani jami’in gwamnati ya kara rura wutar zargin a shafin Twitter. Sai dai bai bayar da wata hujja ta zahiri ba.

Galibin bayanan da aka yi a ranar  4 ga Maris sun yi hannun riga da sakamakon nazarin kwakwaf da aka yi, kuma ba su yi wani tartibin bayani abin dogara game da cutar ba. Wata jarida a Amurka mai suna USA TODAY ta yi kokarin magana da wanda ya fara wallafa zargin biyu mai suna Larry Romanoff, domin ya yi karin haske game da ikirarin, sai dai ba a iya samunsa ba.

Me masu binciken suka gano cewa  COBID-19 ta samo asali daga China

Masu binciken da suka yi nazarin yaduwar cutar sun yi ittifakin cewa mai yiwuwa ta samo asali ne daga “kasuwar dabbobin ruwa masu rai” da ke birnin Wuhan na China. Sai dai ba su kawar da yiwuwar cewa wani mai dauke da ita ne ya shigo da kwayar cutar cikin kasuwar ba, wanda hakan ba zai nuna cewa daga wata kasa aka shigo da ita ba.

Hukuncinmu: Karya ce kawai

Makalar da take karakaina a soshiyal midiya cewa cutar ba ta samo asali daga China ba. Mun yanke hukunci kan ikirarin a matsayin zuki-ta- malle ce kawai, saboda babu wani bincike ya karfafa shi. An samu ittifaki a tsakanin masana da ke gudanar da bincike kan kwayar cutar cewa ta fara yaduwa ce daga kasuwar sayar da abincin teku mai suna Huanan Seafood da ke birnin Wuhan a China.

Likitoci na zabar wanda zai rayu da wanda zai mutu a Italiya

Likitocin da ke gaba-gaba wajen yaki da cutar Kurona a kasar Italiya sun ce suna fuskantar wani mummunan hali na zabar wanda zai rayu ta hanyar yi masa magani da wanda za su kyale ya mutu . Shugaban Sashen Musamman a Asibitin Bergamo da ke Arewacin Lambordia, Dokta Christian Salaroli, ya shaida wa jaridar Corriere della Sera cewa: “Idan mutum ya kai tsakanin shekara 80 zuwa 95 kuma yana cikin tsananin yanayi na cutar, to watakila ba za ka iya ci gaba da ba shi kula ba. Akwai kalamai masu matukar tayar da hankali, amma kuma a zahiri su ne gaskiyar magana. Ba za mu iya yin abin da za ku kira mu’ujiza ba.”

Cutar Kurona ta yi muni sosai a Italiya, an samu mutuwar mutum 2,500 daga cikin mutum 31,500 da suka kamu da cutar.

Masu cutar Kurona sun doki  jami’an lafiya sun tsere

Jami’an lafiya a Arewacin Afghanitan sun ce gomman mutane da ake tsare da su kan zargin suna dauke da cutar Kurona sun gudu, bayan sun lakada wa jami’an lafiya duka Jami’an sun ce akalla marasa lafiya 36 ne suka tsere tare da taimakon ’yan uwansu.

BBC ya ruwaito cewa ma’aikatan lafiyar sun tabbatar wadanda suka gudun sun yi haka ne bayan sun ci karfin jami’an da ke tsare da su a yankin Herat da ke makwabtaka da Iran. Wani jami’in lafiya a kasar ya ce dukkan wadanda suka gudun sun dawo ne daga Iran. Kuma akwai mutun daya daga ciki da aka tabbatar yana dauke da cutar. An tabbatar mutum 21 na dauke da cutar a Afghanistan kawo yanzu.

China ta fusata da Trump ya kira cutar Kurona “’yar China”

China ta fusata bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya kira cutar da “’yar China.” Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Geng Shuang, ya gargadi Amurka a kan ta je ta ji da matsalolin da ke gabanta kafin ta tsangwami China. A makon jiya ne Geng Shuang, ya yada wani labari da ke zargin dakarun Amurka da kai cutar yankin. Wannan zargi ne ya sa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya bukaci China ta daina yada abin da ba ta da tabbas a kansa.

A ranar Litinin da ta gabata ce, Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na Twitter inda ya bayyana cutar  Kurona a matsayin ’yar China.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadi a kan danganta cutar da wani ko wata kungiya saboda gudun tsangwama. Sakon na Trump ya ya harzuka mahukuntan China, Geng Shuang, ya ce wannan ba daidai ba ne domin zai iya janyo wa China tsangwama. Ya ce, “Muna bukatar Amurka ta gyara maganarta a kanmu, sannan ta daina yi mana kazafi.”

Kamfanin Dillancin Labarai na kasar China Dinhua ya ce kalaman Trump alamu ne na wariyar launin fata da nuna kabilanci.

Ibory Coast ta hana Amurkawa da Faransawa shiga kasarta

Ibory Coast ta bi sahun kasashen Afirka da suka dakatar da shigar baki ’yan kasashen waje daga wuraren da cutar ta fi tsanani. A wata sanarwa da hukumomi suka fitar a farkon mako, sun ce dakatarwar ta shafi kasashen da suke da masu dauke da cutar fiye da 100 ne kawai, kuma ta wucin-gadi ce. Kasashen sun hada da Amurka da Faransa da Birtaniya da kuma yawancin Nahiyar Turai.

Nan da kwanaki masu zuwa, ’yan asalin kasar ne kawai da masu zama dindindin a cikinta za a bari su shiga daga wata kasar, su din ma sai an killace su na tsawon mako biyu a lokacin da suka isa kasar. Hukumar tsaro ta kasar da Shugaba Alassane Ouattara ke jagoranta, ta kuma bayar da umarnin rufe makarantu da jami’o’i tun ranar Talata har tsawon kwana 30.

Sannan za a rufe mashaya da wuraren shakatawa daga tsakar daren shekaranjiya Laraba, har tsawon kwana 15, amma akwai yiwuwar sake duba matakin. An kuma hana duk wani taro da ya wuce na mutum 50, kamar wasanni da tarurrukan al’adu, daga tsakar daren Larabar har tsawon kwana 15. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an samu masu dauke da cutar uku a Ibory Coast, sai dai babu mutuwa zuwa yanzu.

Babban Limamin Ghana ya bukaci Musulmi su bi umarnin daina zuwa masallaci

Ofishin Babban Limamin Kasar Ghana Dokta Osman Nuhu Sharubutu, ya bukaci al’ummar Musulmin kasar su bi umarnin Shugaba Nana Akufo Addo wanda ya umarci dakatar duk wani taron jama’a da suka hada da haduwa a masallatai da coci-coci da zaman makoki da jana’iza da aure da duk wani taron da ke hada jama’a har zuwa mako hudu don dakile yaduwar cutar.

Ghana dai na cikin kasashen Afirka 31 da cutar Kurona ta bulla.

Ta shiga dukkan jihohin Amurka 50

Cutar ta bulla a dukkan jihohin Amurka 50, yayin da Jihar West Birginia ta bayyana rahoton bullar cutar a ranar Talata. Da yake bayar da sanarwar bullar cutar, Gwamnan Jihar, Jim Justice, ya ce: “Dama mun san tana kan hanya.”

Birnin New York City, ya ce yana tunanin kulle birnin baki daya irin yadda yankin San Francisco Bay area ya yi. Zuwa yanzu mutum 108 ne suka mutu daga cutar a Amurka, inda aka tabbatar sama da 6,300 sun kamu da ita.

Tarayyar Turai za ta hada kudi don yakar masassarar tattalin arzikin da cutar za ta haifar

Ministocin Kudi na Tarayyar Turai sun yi alkawarin hada karfi domin yakar masassarar tattalin arziki da cutar za ta haifar. Kowace kasa ce za ta yanke shawara kan irin matakan da za ta dauka a kasarta; amma hukumar Tarayyar Turai ta ce sama da Dala biliyan 130 aka yi alkawarin samarwa kawo yanzu. Tuni gwamnatin Birtaniya ta yi alkawarin Dala biliyan 15 a matsayin tallafi don bunkasa kasuwanci.

Gwamnatoci ba sa katabus don dakile cutar – WHO

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce gwamnatocin kasashe da dama ba sa yin abin da ya kamata wurin dakile cutar Kurona. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce ya kamata a fito da wasu hanyoyin gwaji, kuma duk wanda aka tabbatar na dauke da cutar dole ne a killace shi a kuma gano duk wanda ya yi hulda da shi.

Dokta Tedros ya bukaci kasashe su kwaikwayi salon kasashe kamar China da Koriya ta Arewa, inda ya ce sun nuna cewa za a iya cin karfin cutar.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya