✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birgimar bagararwar Baffan-rawa

Birgimar burgar buguwa Bambamin bagararwa Bani-banin bilinbituwa Bakancen baubawa Basarwar Baffan-rawa   Baffan-rawa An dai daki garwa An ji dadin kwankwadar gahawa Ana ta kada…

Birgimar burgar buguwa

Bambamin bagararwa

Bani-banin bilinbituwa

Bakancen baubawa

Basarwar Baffan-rawa

 

Baffan-rawa

An dai daki garwa

An ji dadin kwankwadar gahawa

Ana ta kada kararrawa

Karajin karairayi ke ta kuwwa

 

Basajar basarwa

Babbar farautar farawa

Bahaushen haushin furtawa

Balullubar farar kawa

Balbelar fuka-fukin filfilawa

 

Salon sunkutar salwa

Sharrin sha’awar shewa

Sama-saman samamen shamuwa

Sharbar sawarmar shirwa

Surar dan tsako shaho yai shakuwa

 

Danbotonku ya subuto

Ku hau kan garu a kusanto

A bar batun wato-wato

Dukiyar mabarnata aka kwato

Bera da gafiya ne suka sassato

 

Kura ce suka kwanto

Dole ai musu kwarmato

Miyagu an rasa koto

Da an take talaka da kofato

Sai mu fasko a fahimto

 

Lullumin lumana za mu zamto

Kyawawan ta’adu an hakaito

Muguntar mugga an ruwaito

Rayuka su zam ceto

Mu hada karfi a firfito

 

’Yan rawar yanyawa

Yatsinen yamutsawa

Yari-yarin yarawa

Yangar  yakicewa

Yuyuyun yagalgalewa

 

Karakainar  karawa

Karma-karmar kwakumewa

Kumbiya-kumbiyar kundumewa

Kurbe-kurben kurbewa

Kankambar kai-kawon katantanwa

 

Haramben hargitsewa

Hargagin hange-hangen hangamewa

Haka-hakan haukacewa

Hutsancin hautsinewa

Hayagagar hankoron hadidiyewa

 

Tallace-tallacen tattalin tallatawa

Turka-turkar takurawa

Togaciyar takarkarewa

Tulelen tulun tuttulewa

Talalar tunkudewa

 

Dauke-dauken daddakowa

Dokin dagawa

Damarar daurewa

Dundume kururun dumamewa

Dumamen dundumewa

 

Motsin mutsuttuke matsabbai

Make-maken kwasar kwabbai

Tudu da kwarin kwazazzabai

Ba na kwanaren karkatar da dalibai

Sai  yawan zubo jawabai

 

Usainin-babajo

Ka fasko masu rawar banjo

Da suka tara kudin ajo

Suka gwabje  su gwarjo

Suka cutar da su Hajo

 

Aminai

Kar a yaudareku da aninai

Kun dai ji haushin karnai

Burinsu tara taro da nai

Dode na-mujiyar gannai

 

Sun sulale da sulalla

Sun ga galala

Sun dinka galleliyar galila

Sun bar talakawa na lala-lala

Sun tsala wa al’umma bulala

 

Ba sauran kulunboto

Ballantana su wane su karkato

Wai dukiya za su wafto

Masar al’umma saura toto

A kiyaye dai kowane loto

 

Na ji batun teburin mai shayi

Kowa ya hau bisa layi

Mu daina layi

Mu sha maganin laulayi

Waskiya ta sha kayi

 

A kula kowa-da-kowa

Mu daina kokowa

Al’umma ta daina tsiwa

Miyagu nai muku kuwwa

Daddawar adawar dawan duhuwa

 

Mugun yai makuwa

Maganganu yai ta jefawa

Tsigarewar tsiwa

Baba dai yai musu tsawa

A bar su sui ta tsuwwa

 

Nai muku kalami

A kauce wa jimami

Da salallami

Kar magabta su daure dami

A zo ai ta bambami

 

Mui wa knmu masalaha

Kar ai mana dararraku hahaha

Wai an samu ahaha

In komai yai arha

Sai mu ji dadin raha

 

 

‘Juma’atu babbar rana, Laraba ta-bawa ranar samu, a cewar mai bara’

Ni dai na jiyo bambamin batutuwan Baffa-rawa, inda ya tallatatsiwar tsiya-tsiya ga jam’iyyar tsintsiya ta Baban-burin-huriyya, kamar yadda aka baje mana a fuskar Amintaciyar jaridar kasar Haurobiya ta Juma’ar da ta arce, wato ranar madambaci ga watan Dashen-Baba na shekarar dubu karamin lauje da sili da tukunyar dambu. Wannan dalilin ne ya sanya darasin wannan mako ya bi kadin RUGUGIN RAWAR BAFFAN-RAWAR MAI DANBOTO DA SANDA JIRGE, musamman ma bisa yunkurinsa na sake jirga gama-garin al’ummar Haurobiya.

Akwai yiwuwar wannan makaranta ta Dodorido ta jefa azargagiyar zargi kan Baffan-rawa wajen lalata tarairaya da biyayyar masu fuka-fukin tashi, har ta kai yau babu abin da ake ta tsuwurwurtawa a birnin Shehu Mujadaddi illa TAMBELEN TUMBIN WULLI. Domin ga dukan alamu su suka rudi Gwamna gwarangwam ya tsallaka dan boton jirga talakawan kasar nan, har ma ya yi hankoron taka-karan dannin danniyar jan ragamar al’ummar kasar nan.

Ko ma dai wace irin manufa ta sanya Baffan-rawa yake ta rangajin rungumar tsiyatakun tsuke jama’a a tsukuku, domin su dajin wawurar waftar waku, mun san dai BANZA BA TA KAI ZOMO KASUWA. Ko dai Iro Mugun Madambaci ya kai wa Baffan-rawa farmaki ne? To babu mamaki matukar hakan ta kasance, tunda na ji cewa shi ma ya kwashi rabonsa, daga lalitar kasa da Samun-bom-da-sauki ya dan jinka wa jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Kuma sanin kowa ne damin matsabban an ware su ne don sayen na’urorin artabun ayyukan BARADEN BINDIGA, don tukarar masu haramta  Bobo-da-kwambon bokoko.

Haurobiyawa idan kun ga mutum shi ba dan jinjiri ba, shi ba a cikin tawagar masu raye-raye da kade-kade ba yana ta taka rawa,ku yi kuwwa a zo a duba kwanyarsa. Kai ’yan makaranta in kun gan ni ina rawa babu gaira, ba dalili, to ku yi mini tashen KAI MALAM KA YI RAWA, ni kuwa sai in ce muku BAN YI ba!