Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Biyan batagari aka yi suka yi wa Buhari ihu- Garba Shehu

Malam Garba Shehu

Biyan batagari aka yi suka yi wa Buhari ihu- Garba Shehu

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, ‘yan siyasa ne suka dauki hayar batagarin da suka yi wa shugaba Buhari ihu ranar Laraba a Maiduguri a lokacin ziyarar da ya kai na jaje a Jihar Barno.

A zantawarsa da sashen Hausa na BBC a ranar Alhamis, Malam Garba Shehu ya shaida cewa yana cikin tawagar da suka je ziyarar kana batagari ne kadai suka yi ihun.

“Ina cikin tawagar tun daga tashar jirgin sama har zuwa fadar Shehun Borno, duk jama’a da suka hallara domin tarbar shugaban kasa sun fito kwansu da kwarkwata suna lale marhabin, batagarin ne kadai suka yi ihun “ba ma so.” In ji shi.