✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biyan Jihar Kogi kudi yanzu rashin gaskiya ne – PDP

Kudin da Gwamnatin Tarayya ta kudiri biyan Jihar Kogi ya haifar da takardama a tsakanin Jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adwaa ta PDP.…

Kudin da Gwamnatin Tarayya ta kudiri biyan Jihar Kogi ya haifar da takardama a tsakanin Jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’iyyar adwaa ta PDP.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nemi a biya Jihar Kogi wani tsohon bashi da take bin Gwamnatin Tarayya da ya kai Naira biliyan 10 na wasu ayyukan tarayya da gwamnatin jihar ta taiwatar.

Amma Jam’iyyar PDP ta ce bai kamata a biya kudin a wannan gaba da ake shirin yin zaben Gwamna a jihar ba, tana zargin cewa ana so ne a bai wa Gwamna Yahaya Bello kudin don yin magudin zabe.

Tuni Gwamnatin Tarayya ta mika bukatar biyan wannan kudi gaban Majalisar Dattawa.

Wani jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Baba Sule ya shaida wa BBC cewa idan APC ta taki gaskiya me ya sa tuntuni ba a biya kudin ba?

Ya kara da cewa “Gwamnan da zai yi zabe nan da wata guda za a dauki wadannan makudan kudi a ba shi, wani salo ne don a yi magudin zabe da bai wa ’yan bangar siyasa’.’

Baba Sule ya ce a baya tsohon Gwamnan Jihar Idris Wada an taba batun ba shi kudi amma da yake lokacin zabe ne sai aka dakatar da nasa, don haka idan gwamnati za ta yi adalci bai kamata a bada kudin ga gwamnatin Yahaya Bello ba. Amma a bangaren gwamnatin jihar ta bakin Sakataren Watsa Labaran Gwamnan, Mohammed Onogwu ya ce kudin ba ya da alaka da zabe.

“A watan Janairun bana, lokacin da aka gabatar da irin wannan bukatar domin jihohin Bauchi da Kogi su amfana babu zaben Gwamna a Jihar Kogi. Wadansu ’yan majalisa ’ya’yan Jam’iyyar PDP ne suka hana a ba da kudin. Saboda haka idan muka samu kudi za mu samar da abubuwan more rayuwa ne,’’ inji Mohammed Onogwu.