✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biyayya ita ce sirrin zaman aure – Hajiya Maryam Muhammad Hassan

Hajiya Maryam Muhammad Hassan ita ce mai makarantar Sabi’ul Rashad  wadda yake nufin ‘hanyar shiriya’ da ke Yola na Jihar Adamawa. Ta kasance cikin wadanda…

Hajiya Maryam Muhammad Hassan ita ce mai makarantar Sabi’ul Rashad  wadda yake nufin ‘hanyar shiriya’ da ke Yola na Jihar Adamawa. Ta kasance cikin wadanda ke yi wa mata fada da sanya su a kan hanya a lokacin zuwa Hajji ta gwamnatin Jihar Adamawa wadda a cewarta ta je aikin hajji har sau goma. Ta yi saukar Alkur’ani tun tana ’yar shekara 10.  A wannan zantawar da ta yi da Aminiya, ta yi bayani a kan sirrin rike miji da kuma zaman aure.

                                

Tarihinta:

Sunana Maryam Muhammad Hassan, ni haifaffiyar Yola ce a Jihar Adamawa. Ni matar aure ce. Na yi karatun firamare a Sanda firamare da ke cikin garin Yola. Bayan na gama karatun firamare sai aka yi mini aure. Bayan na haifi ’ya’ya biyar sannan na je makarantar Islamiyya. Ban gama makarantar Islamiya ba sai aka bude fannin koyon addini na mata da maza a Kwalejin Horar da Malamai ta Mata  (WTC) sai na ta fi can. Sai na shiga makarantar koyar da larabci da addini na sakandare a nan na yi aji na daya har zuwa na karshe. Sai na ji karatu ya yi dadi, sai na kara karatun Diploma a Jami’ar Bayero ta Kano (B.U.K) inda na karanci Larabci da Hausa da kuma karatun addini. Bayan na gama, sai aka bude mana Jami’ar Ilorin a Yola, ina jin haka sai na wuce can. Daga nan sai na yi sha’awar bude makaranta. Akwai ’ya ta da na sanya ta yi gwajin shiga makarantar Darul ‘arkam sai abin ya ban mamaki da bat a ci ba saboda ina koyar da mata da yara a gida. Kuma duk wasanninta ma karatu n,. hakan ya sanya na yi zuciyar bude makaranta. Sai na sanar a unguwa da kuma a gidan rediyo na soma karantar da yara na nursery. Ina tsammanin yara biyu zuwa uku sai na ga an cika. Masha Allah daga tun daga matakin Islamiyya har ta zama babbar makaranta.  A yanzu da muke magana na yaye daliban sakandare kashi biyu kuma wadansu suka samu damar tafiya jami’a. 

 

Wanda na fi shakuwa a tsakanin iyayena:

Mahaifina ya rasu hakan ya sa ban shaku da shi ba. Na fi shakuwa da mahaifiyata domin na fi zama da ita fiye da zaman da na yi da mahaifina. Ita ma daga baya Allah Ya karbi rayuwarta.

 

Halayyar da na gada daga iyayena:

Alhamdulillah! iyayena duk masu son karatu ne sannan mahaifiyata na son natsuwa a gidan aurenta har ya zamana ba ma fita sai da izininta. A kullum tana fada mana cewa kashi saba’in da biyar a rayuwar aure ibada ce kuma da hakuri wannan na daya daga cikin kalmominta da nagada.

 

Farin cikin zama uwa:

Wannan ranar dai ba ta misultuwa sai dai mutum ya fadi kadan daga cikin farin cikin da ya ji. Na farko ban taba na zauna ban yi bacci a rayuwa ta ba sai a wancan lokacin. Don haka babu farin cikin da zai wuce wannan.

 

Sirrin zaman gidan aure:

Abu na farko shi ne bin doka, abin nufi a nan, shi ne duk abin da miji ya tsara in dai har bai ci karo da shari’ar Musulunci ba in kina musulma, sai ki bi dokar don a zauna lafiya. Abu na biyu, mace ta kasance tana da tsafta a kowane lokaci. Tsafta a nan ana nufin tsaftar abinci da jiki da kuma na gida. In har mace na da wadannan abubuwan da na lissafo, insha Allahu ana kyautata    zaton samin zaman lafiya. Yana da kyau mace ta rufe sirrin mijinta wannan shi ne sirrin zaman gidan miji.

 

Yadda na tafiyar da harkar karantarwa da kula gida:

Da farko sai da na hada da tawakkali da hakuri. Domin karantun na yi shi ne da girma ga kuma haihuwa ga aikin gida. A lokacin ba a samo min mai aiki da za ta taya ni aiki a gida ba. Idan na tashi karfe uku na dare, na riga na jika kayan da suka yi amfani da shi sai na kwanta. Idan na tashi cikin dare, sai na wankesu tas na shanya, sannan na fito na shiga kicin na dora abincin karyawa da na rana. Ina girka kayan karyawa, ina dafa abincin rana. kafin takwas zuwa tara sun tafi makaranta ni ma na tafi tawa tare da goyon daya daga cikinsu. Ina dawowa sai na aza hijabina a kofa sai na dumama wannan abincin da na yi tun da sassafe. Sannan yara sun dawo sai mu hadu mu ci wannan dumamen. Azahar na yi za su tafi karatu, ni kuma a wannan lokacin sai na fara shirin girkin dare. Ina gama abincin daren karfe hudu saura, sai na kwashe na share gida domin yara masu karbar karatu za su zo wajena. Wadansu yaranma a kicin nake karantar da su saboda yawa.bayan mun yi Sallar Maghariba da Isha’I, sai mata na unnguwarmu su ma za su zo daukar darasi a haka na yi ta wannan rayuwar.

 

Abincin da nafi so:

Ina son cin tuwo kowane iri ban da na dawa da miyar yauki. Sannan ina cin danyen kifi.

 

kasar da nafi sha’awar zuwa hutu:

Babu inda na fi sha’awar zuwa hutu kamar Saudi Arabiya, domin duk gurin hutu akwai a wannan garin. Bayan hutawa ga ibada.

 

Nasarorin da na samu a rayuwa:

Alhamdulillah, nasara na farko dai da na sa wannan karatu a gaba, na sanya ’ya’yan mutane sai nawa ma suka zo suka yi karatu. A cikin ’ya’yana mata hudu duk za su hada Al-kur’ani yanzu karamar ne take kokari. A cikin mazan ma su ma sun gama Islamiya.  Sannan a kan haka ne gwamnatin Jihar Adamawa take daukar nauyina kowace shekara  zuwa Hajji domin fadakar da mata mahajjata wadanda suka fito daga Jihar. Aikin hajjin da na yi a bara (2017) zan iya cewa shi ne aikin Hajji na 10 a rayuata.. Sannan makarantar da na bude ta habbaka har zuwa matakin sakandare wacce ake karantar da su ilimin addini da na zamani. Kuma ana rubuta jarabawar fita daga sakandare (WAEC) duk a makarantar. Wadannan kadan kenan daga cikin nasarorin da na samu.

 

Burina a rayuwa:

Babban burina a rayuwa shi ne in zama a kowani lokaci na ga ban saba wa kowa ba hatta makwabci. 

 

Kwalliya:

Ina son kitso da lalle da kuma turaren humra

 

 Yadda nake shakatawa:

Idan na yi wanka na yi kitso da lalle sai na kunna tashar Musulunci a talabijin na zauna ina kallo sannan da yamma kuma sai na ta fi Islamiyya.

 

Macen da take burgeni:

 Nana Khadijah matar Manzon Allah (S.A.W) wacce ta nuna masa so da kauna, ta dauki dukiyarta ta taimaka masa har aka habbaka harkar Addini. Sannan Nana A’isha uwar mumunai ita ma tana burgeni saboda Manzon Allah (S.A.W) kafin ya bar duniya ya ce duk ilimi mu kwasa a wajenta. Kuma ina sha’awar na ga mace ta yi shigar musulunci da ilimi.

 

Shawara ga matasa:

Matasa su yi kokari su yi karatu. Saboda karatu ba ya rubewa. Su hada karatu da sana’ar hannu komai kankantarta. Matasa su hada da addini. A nemi sana’a a yi karatu.

 

Abubuwan da nake so ana tunani da shi ko bayan raina:

Ina son a tunani da irin karantarwar da na yi daga  alif har zuwa karshen abin da na karantar. Ko a ina dalibai na suke da’yan uwa, ina so suna tuna ni da wannan.