Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Boko Haram: An kashe mutum 10 da kone gidaje 100 a Borno

Akalla mutum 10 aka kashe da raunata wasu da dama, a wani sabon hari da ake zargin ‘yan Boko Haram sun kai unguwar Molai wajen garin Maiduguri babban birnin jihar Borno.

An kai harin ne a cikin unguwar Molai da ke karamar hukumar Jere a yammacin jiya Talata. Maharan sun kona sama da gidaje 100 a kauyukan Maiboriti da Molai.

ADVERTISEMENT

Wani mazaunin garin mai suna Mallam Isa Kagama ya bayyanawa majiyarmu cewa, wannan harin ya yi sanadiyyar rasa gidajen su bakwai.

 

ADVERTISEMENT