Aminiya

Boko Haram: Dalilin da muka tunkari malaman Saudiyya da ’yan tauri – Gwamnatin Borno

Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara

Gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar da cewa malamai suna gudanar da addu’o’i da Dawafi a Kasa Mai tsarki don rokon Allah Ya kawo karshen matsalar Boko Haram a jihar da Arewa maso Gabas.

Mai bai wa Gwamnan Jihar Borno Shawara kan Harkar Watsa Labarai, Malam Isah Umar Gusau ya tabbatar wa wakilinmu haka a garin Maiduguri.

ADVERTISEMENT

Ya ce “Abin da ke faruwa, ganin matsalar Boko Haram ta-ki-ci-ta -ki-cinyewa, duk da jami’an tsaro suna iya bakin kokarinsu dona dakile wannan lamari, Borno da wannan yanki na bukatar samun cikakken zaman lafiya kamar da, shi ya sanya Gwamna ya yi tunanin samun malamai a kowane lokaci kuma a ko’ina don gudanar da addu’o’in. Kuma gaskiya ce, Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya sanya malamai yin addu’o’i da gudanar da Dawafi da nufin Allah Ya kawo karshen matsalar Boko Haram a Borno da yankin Arewa maso Gabas, kama tun daga nan Jihar Borno har zuwa Kasa Mai tsarki amma abin da ya faru a Kasa Mai tsarki shi ne, akwai malamai su 30 kuma ’yan asalin Najeriya ne, 17 ’yan asalin Jihar Borno ne, a yayin da sauran suka fito daga jihohin Katsina da Sakkwato da Bauchi kuma dukkansu suna zaune ne a can Saudiyya. Duk da cewa a farko Gwamna ya bukaci yin addu’o’i to amma su malaman sun dauki alkawarin hadawa da Dawafi a kullum ba tare da an ba su ko kwabo ba, domin sun ce wannan  ita ce gudunmawar da za su iya bayarwa don samar da dawwamammen zaman lafiya a Borno da Arewa maso Gabas da kasar baki daya.

“Wannan addu’a a ko’ina ana yin ta, don haka ba gaskiya ba ce da ake cewa an biya wadancan malamai. Kuma ba gaskiya ba ce da ake cewa suna yin wani sidabaru ko layar bata, to amma kuma hikimar yin addu’o’in ita ce ta al’ummar Jihar Borno da yankin Arewa maso Gabas da kasa baki daya su samu dawwamammen zaman lafiya, a kuma kawo karshen wadannan fitinu da suka dabaibaye mu, wannan shi ne kawai.”

ADVERTISEMENT

An ruwaito Gwamna Babagana Umara yana cewa za su gayyato maharba da ’yan tauri ciki har da masu layar zana da sauran asirrai don tunkarar dazuzzukan da ’yan Boko Haram suke da maboya don murkushe su.

Gwamnan ya ce “Bai kamata a bari ta’asar Boko Haram ta yi ta ci gaba da aukuwa ba, dole ne a nemo hanyoyin dakile ta. Don haka ne muke daukar matakai daban-daban don kawo karshen lamarin, duk da cewa jami’an tsaro suna iya kokarinsu to amma ba za mu nade hannu mu bar su su kadai ba. Dole ne mu taimaka da namu karfin ko iko don ganin an kawo karshen lamarin kowa ya huta.”

Wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Ibrahim wanda ya goyi bayan sanya malamai su yi addu’a kan lamarin, ya nanata bukatar gudanar da addu’o’i a kowane lokaci don neman sauki kan halin kuncin da al’ummar yankin ta tsinci kanta a ciki. Ya ce “A gaskiya halin da kasarmu ta shiga na tashin hankali da rashin zaman lafiya, yana da kyau a yawaita addu’o’i kuma a bukaci wadansu  su taimaka da yin addu’ar a ko’ina suke balle a Harami don neman biyan bukata daga Allah. To amma ba daidai ba ne a sanya wani kagaggen abu ko fararren abu ko kuma bidi’a cikin lamarin ba.”

Ya ce ba daidai ba ne a yi amfani da masu layar zana ko ’yan tauri don yaki da Boko Haram, inda ya ce Musulunci bai amince da layar zana ba kuma bai yarda da tauri ba, don haka amfani da masu wadannan abubuwa ba daidai ba ne.

Sai dai Sheikh Malam Goni Umara, bayan ya bayyana muhimmancin sanya wani mutum na daban ya taya wanda ke cikin matsala da addu’a a lokacin da yake da bukata a wajen Ubangiji. Ya ce “Ka sa wadansu malamai su yi maka addu’a da rokon Allah Ya biya maka bukatarka ko a roke Shi Ya yaye wata damuwa ko matsatsin da aka shiga, ba laifi ba ne.”

Kuma ya ce ana iya amfani da masu duk wata dabara ko wani abu da zai taimaka wajen yaki da Boko Haram, kamar masu layar zana da ’yan tauri.