Search
Subscribe
Boko Haram ta sake kashe mutum 65 a Borno

Mahara

Boko Haram ta sake kashe mutum 65 a Borno

Bayan mako daya da wasu mutane suka yi arangama da ‘yan kungiyar, inda suka kashe ‘yan kungiyar 11 tare da kwace makamai da dama, mayakan Boko Haram din sun mayar da martani yayin suka kashe a kalla mutum 65 a karshen wannan mako.

Mafi yawan wadanda aka kashe suna hanyar su ne na dawo wa daga wajen jana’iza a wani kauye da ke Karamar Hukumar Nganzai a Arewacin jihar Borno.

Shugaban Karamar Hukumar Nganzai Mohammed Bulama, ne ya bayyanawa Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum, hakan lokacin da Gwamnan ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe a Gajiram Hedkwatar Karamar Hukumar.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin