Boko Haram ta saki ma’aikatan agaji 5 da ta kama

Ma’aikatan agajin nan biyra da Boko Haram ta sace a ranar 22 ga  Disamban bara, sun samu ’yancin a shekaranjiya Laraba, kamar yadda wata majiyar tsaro ta bayyana wa Aminiya.

Ma’aikatan biyu mata ne, inda saura uku maza ne kuma ’yan Boko Haram sun sace su ne bayan sun yi wa motar da suke ciki kwanton bauna, a kan hanyar Monguno.

A cewar majiyar da ta nemi a sakaya sunanta sakin ma’aikatan agaji ya biyo bayan wani shiri ne da jami’an tsaro na sirri suka aiwatar, inda lamarin ya kasance wani abin farin ciki a Jihar Borno.

Majiyar ta ce biyu daga ciki ma’aikatan kungiyar bada agaji ta ALIMA ne, daya kuma na Solidarity International, sai kuma daya daga IOM, sai kuma daya daga Red Cross.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya