✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta yi amfani da yara 83 wajen kunar bakin wake a bana – UNICEF

  Asusun Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF), ya ce kungiyar Boko Haram ta kara yawan amfani da kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin…

 

Asusun Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF), ya ce kungiyar Boko Haram ta kara yawan amfani da kananan yara wajen kai hare-haren kunar bakin wake a bana.

Asusun UNICEF ya ce, kungiyar Boko Haram din ta yi amfani da kananan yara 83 wajen dana musu bama-bamai suna kai harin kunar bakin wake a bana, ciki har da yara mata 55 da yara maza 27. Kuma a cewar Asusun UNICEF galibin yara suna kasa da shekara 15 ne, yayin da daya ma jariri ne da aka goya masa bam din aka goya shi a bayan wata budurwa.

Adadin na bana ya yi kusan ninka na bara sau uku, inda a bara Boko Haram ta yi amfani da kananan yara 30 a matsayin ’yan kunar bakin wake.

“Yin amfani da kananan yara a irin wadannan hare-hare yana kawo karin zargi da tsoro ga yaran da aka sako ko aka ceto ko suka kubuta daga Boko Haram. Sakamakon haka, yara da dama da suka iya kubuta suna fuskantar rashin amincewa daga jama’a a lokacin da suke neman komawa cikin dangi wanda hakan ke kara munin halin da suke ciki,” inji sanarwar UNICEF.

“Wadannan yara ba su suke shirya wannan tu’annati ba, su ma ana cutar da su ne,” inji Marie-Pierre Poirier, Daraktar Yankin Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya na Asusun, wadda ta ce a watan Afrilu, “Tilasta su ko yaudararsu su aikata wannan danyen aiki ya yi matukar karuwa.”