✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Borno

Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum ya tabbatar da mutuwar mutum 81 a hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a Arewacin jihar. Zulum ya ce…

Gwamnan Jihar Borno Babagana Zulum ya tabbatar da mutuwar mutum 81 a hare-haren da kungiyar Boko Haram ta kai a Arewacin jihar.

Zulum ya ce mayakan kungiyar sun kuma yi garkuwa da Hakimin garin da wasu mutum shida a hare-haren na ranar Talata.

Ya bayyana wa ‘yan jarida cewa, “Ba mu gama tattara bayanai ba, amma kun ji daga bakinsu cewa sun binne mutum 49 a wannan makabartar.

“Wasu mutum 32 kuma danginsu sun tafi da gawarwarkinsu. Kawo yanzu sun gano gawarwaki 81 ke nan,” inji gwamnan.

Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi da wasu mutun shida
Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno a ziyarar ta’aziya ga mutan Gubio

Da yake ziyarar ta’aziyya a kauyen Felo da ke Karamar Hukumar Gubio, Gwamnan ya bayyana alhini tare da neman sojoji su murkushe kungiyar.

Aminiya ta ruwato yadda mayakan kungiyar Boko Haram suka kashe mutum 69 a lokaci guda a kauyen Foduma Kolomaiya a Gubio.

Mayakan sun kuma sace dabbobi tare da lalata dukiya mai tarin yawa a kauyen kwana biyu bayan Babban Hafsan Mayakan Kasa Tukur Buratai ya bar jihar inda ya jagoranci yaki da kungiyar.

Maharan sun shafe awa biyu suna cin karensu babu babbaka da tsakar rana a kauyen inji shaidu.

Sa’o’i kadan bayan jana’iza, maharan suka kara komawa kauyen inda suka sake bude wuta a kan jama’a.