✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta yi wa fararen hula yankan rago

‘Yan Boko Haram sun kashe fararen hula 38 ciki har da kananan yara da mata a karamar Hukumar Nganzai ta jihar Borno. Maharan na safiyar…

Yan Boko Haram sun kashe fararen hula 38 ciki har da kananan yara da mata a karamar Hukumar Nganzai ta jihar Borno.

Maharan na safiyar Asabar sun yi wa mutane yankan rago, suka kona gidaje sannan suka saci dabbobi a kauyen Usmanati Goni.

Wani jami’in tsaron sa kai ya shaida wa wakilinmu cewa mayaka cike da motoci sun kuma kai hari a daidai lokacin a Karamar Hukumar Monguno.

An yi wa mutane yankan rago

Game Usmanati Goni, “‘Yan ta’addan sun kashe fararen hula kusan 40, har da mata da kananan yara da ba su ji ba, basu gani ba.

Ya ce, “A safiyar wasu mazauna sun tsere zuwa kauyen Gajiram, amma da jami’anmu suka raka su suka koma sai suka iske an yi wa ‘yan uwansu yankan rago an kona gidaje.

“Ba za ta yiwu a yi ta tafiya haka ba dole gwamnati ta dauki mataki. Kasa da kwana biyar da muka rasa mutane 81 an kara kashe wasu kusan 40. Abin ya yi yawa”, inji shi.

Barnar Boko Haram a Monguno

A safiyar Asabar din, mayakan kungiyar suka kai hari a garin Monguno, Hedikwatar Karamar Hukumar Monguno suna ta harbe-harbe.

Rahotanni sun tabbatar da maharan sun kona ofishin ‘yan sanda suka kuma saki wadanda ke tsare.

Sun kuma kai farmaki a wata cibiya ta Majalisar Dinkin Duniya inda suka kona motoci.

Sojoji sun kawo dauki

Majiyoyinmu sun ce sojoji sun shawo kan harin na Monguno wanda ya dau tsawon awa biyu.

Mayakan na kokarin kwace garin ne sojojin Najeriya suka far musu ta kasa da kuma jiragen yaki.

Bayan sojoji sun fatattaki mayakan ne daruruwan ‘yan Monguno suka fito kan tituna suna murna.

Wani jami’in agaji ya ce, “Mun shiga tashin hankali na awanni amma yanzu muna cikin aminci. Mutane sun cika tituna suna murna sojoji sun kora shaidanun

“Yanzu kowa na cikin farin ciki an kawo mana dauki kuma sojojin sun kokarta sosai”,  a cewarsa.

Sojoji na bin sawunsu

Wata majiya tsaro ta ce sojoji sun kora maharan da taimakon luguden bama-bamai da jirage, kuma ana ci gaba da bin sawunsu.

“Komai ya lafa, babu damuwa. An murkushe yunkurin nasu, amma ana bin sawu domin tantance yawan wadanda aka hallaka,” a cewar majiyar.

An kashe mutum 81 a Gubio

Kusan makonni biyu baya mayakan Boko Haram sun kai hari a Karamar Hukumar Gubio inda suka kashe fararen hula 81 da dabbobi sannan suka yi garkuwa da wasu mutane.