✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wasu mayakan Boko Haram sun gudu sun bar iyalansu 72 a Borno

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu mayakan kungiyar Boko Haram da takwararta ta ISWAP sun tsere sun bar iyalansu har kimanin 72 a…

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu mayakan kungiyar Boko Haram da takwararta ta ISWAP sun tsere sun bar iyalansu har kimanin 72 a garin Ngala da ke jihar Borno ranar 10 ga watan Mayu.

Da yake jawabi ranar Alhamis ga manema labarai a Abuja, daraktan yada labarai na hedkwatar rundunonin tsaron Najeriya, Manjo Janar John Enenche, ya ce iyalan sun hada da mata 33 da kuma kananan yara 39 kuma dukkansu yanzu suna karkashin kulawar dakarun Najeriya.

Ya ce a karkashin shirinsu na gyaran hali da ake wa lakabi da ‘Operation Safe Corridor’, rundunar sojan ta sami nasarar gyara halin tsofaffin ‘yan ta’adda akalla 280 wadanda tuni suka koma suka ci gaba da rayuwa a cikin al’umma.

Ya ce daga cikin wannan adadi, 25 an mayar da su Jamhuriyar Nijar, yayin da ake sa ran yaye akalla wasu mutum 603 nan da watan Yuni.

Enenche ya kuma ce rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram ta yi nasarar halaka wasu ‘yan kunar bakin wake su uku da ke shirin tarwatsa sansanin dakarunta a karamar hukumar Gwoza.

Ya kara da cewa dakarun Bataliya ta 144 da Runduna ta 82 da Rundunar Tsaro ta Musamman ta 26 da kuma Bataliyar ta 271 sun sami nasarar kashe ‘yan ta’addar Boko Haram 18 a mako guda da ya gabata.

Ya ce sojojin sun yi nasarorin ne a wasu hare-haren da suka kai yankunan Gamboru-Ngala, Firgi Mubi, hanyar garin Kamale dake karamar hukumar Michika a jihar Adamawa da kuma garin Ngoshe da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Kamaru.

Manjo Janar Enenche ya kuma ce sojojin sun ceto akalla mutane 72 daga hannun ‘yan Boko Haram.

Hakazalika, rundunar a wasu munanan hare-hare ta sami nasarar kashe ‘yan Boko Haram 9 a wani harin kwanton bauna a garuruwan Mainok zuwa Jakana a jihar Borno, inda suka sami nasarar kwato wasu motocin igwa masu dauke da na’urar harbo jirage.

Duk dai a yayin wadannan hare-haren, Eneche ya ce sojojin sun kashe ‘yan Boko Haram 61.

Eneche ya kuma ce rundunar sojin kasa da ke da sansani a Malam Fatori ta kai hari tare da kashe ‘yan ta’adda a garin Tumbun Fulani dake karamar hukumar Abadam duk dai a jihar Borno.

Ya kuma ce rundunar ta sami nasarar kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu da kuma harsasai da dama.