Da Dumi Dumi

Boris Johnson ya sha kaye a Kotun Koli kan dage zaman majalisa

Boris Johnson
Boris Johnson

Kotun Kolin Birtaniya ta yanke hukuncin cewa shawarar da Firayi Ministan kasar Boris Johnson ya yanke ta dage zaman Majalisar Dokoki na tsawon mako biyar, gabanin ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Kotun Kolin ta ce hakan ya saba doka, don haka ba za ta yi aiki ba.

Da take jagorantar yanke hukuncin Mai shari’a Lady Hale ta ce dukkan alkalai 11 da suka jagoranci shari’ar sun yi amanna cewa dakatar da majalisar ya saba wa doka, kuma an yi shi ne domin hana majalisar tsattsefe al’amuran gwamnati yayin da take kokarin fitar da kasar daga Tarayyar Turai.

Tuni dai jagoran Jam’iyyar SNP a majalisar Ian Blackford ya bukaci Firayi Ministan ya gaggauta yin murabus ko su kada masa kuri’ar yanke kauna.

Ya ce wannan tamkar wata girgizar kasa ce, domin ya nuna a fili cewa Firayi Ministan ba ya da ikon dakatar da ayyukan majalisa, saboda haka dole ne ya dauki alhakin abin da ya aikata.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya