✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Brazil ta janye tuhumar da take yi wa Neymar kan fyade

A ranar Talatar da ta wuce ce gwamnatin Brazil ta hannun Babban Lauyanta ta ba da sanarwar  janye tuhumar da take yi wa Neymar kan…

A ranar Talatar da ta wuce ce gwamnatin Brazil ta hannun Babban Lauyanta ta ba da sanarwar  janye tuhumar da take yi wa Neymar kan zargin yi wa wata budurwa fyade.

Budurwar ’yar kwalisa mai suna Najila Tindade Mendes de Souza ta shigar da kara ce a gaban wata kotu a Brazil inda take tuhumar shahararren dan kwallon da laifin yi mata fyade.

Jim kadan bayan ta shigar da karar ce sai gwamnatin Brazil ta kafa kwamitin bincike don gano gaskiyar lamarin da niyyar idan ta samu dan kwallon da laifi zai fuskanci hukunci.

Sai dai a yayin gudanar da binciken ne ta gano ikirarin da budurwar ta yi ba gaskiya ba ne. Hasali ma Neymar da budurwar sun dade suna hulda da juna musamman a shafin sada zumunta na WhatsApp wajen aika wa juna sakonnin soyayya.

Wannan ya sa gwamnatin ta bayar da sanarwar janye tuhumar da ake yi wa Neymar kan zargin fyade.

A wata hira da aka yi da mahaifin Neymar ya bayyana cewa da ma budurwar ta yi wa dansa sharri ne a kokarin bata masa suna ganin ya shahara a fagen kwallon kafa a duniya.  “Mun gode Allah da gwamnatin Brazil ta gane gaskiya kuma muna fata za a hukunta budurwar game da wannan abin kunyar da ta aikata,” inji shi.

Idan ba a manta ba a makon jiya ne wata kotu a Amurka ta wanke shahararren dan kwallon Fotugal Cristiano Ronaldo kan zargin da ake yi masa na yunkurin yi wa wata budurwa fyade a Amurka a shekarar 2009.