Brazil ta shiga halin ni ’ya su

kasar Brazil wacce ta lashe gasar cin kofin kwallon duniya har sau biyar ta shiga matsala bayan da Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta duniya watau FIFA ta fitar da jadawalin jerin kasashen da suka fi kwazo a harkar wasan kwallo a fadin duniya.
A jadawalin, Brazil ce ta 22 daga cikin jerin kasashe 50 da ke sahun gaba.
Idan za a tuna a shekarun baya, Brazil ta rike kambun na daya na tsawon shekaru amma a halin yanzu an samu kasashen da suka sha gabanta a harkar kwallo.
A tarihin kasar, ba a taba samun lokacin da ta samu koma baya a jerin kasashen duniya da Hukumar FIFA take fitarwa ba kamar a wannan lokaci don haka za a iya cewa kasar ta shiga halin ni ‘yasau a harkar kwallo.
Haka kuma yankin Asiya ma ya shiga matsala a jerin kasashen da hukumar ta fitar.  Japan ce ta 35 baya ga kasashen Koriya da Kudu da Australia da ke bin juna a mataki na 40 zuwa sama.
Brazil ce dai za ta dauki nauyin gasar cin kofin Nahiyoyi da aka fi sani da Confederation Cup da ake sa ran farawa a gobe Asabar.  Haka kuma kasar ce za ta dauki nauyin gasar cin kofin duniya a badi idan Allah Ya kaimu.
Ga jerin kasashen da hukumar ta fitar wadanda ke sahun goman farko:
1. Sifen
2. Jamus
3. Ajentina
4. Kuroshiya
5. Holand
6. Fotugal
7. Kolombiya
8. Italiya
9. Ingila
10. Ekwado (Ecuador)

Share