Search
Subscribe
BREXIT: An taka wa Boris Johnson birki

BREXIT: An taka wa Boris Johnson birki

…Za ki iya gaban kanki wajen ficewa – EU

’Yan Majalisar Dokokin Birtaniyya sun yi nasarar dakatar da Firayi minista Boris Johnson daga yunkurin fitar da kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai ba tare da an cimma wata yarjejeniya ba.

’Yan Jam’iyyar Conserbative mai mulki da bangaren Jam’iyyar Labour mai adawa sun kayar da gwamnatin a zaben da ya ba su damar karbe ikon gudanarwa. Yanzu akwai yiyuwar gabatar da kudirin doka da zai jinkirta ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai. Majalisar dai ta kayar da masu goyon bayan Firayi Ministan da kuri’a 328 a yayin da Johnson ya samu kuri’u 301. Sai dai Firayi Ministan ya sha alwashin gabatar da wani kudiri don yin zaben gama-gari.

Boris Johnson wanda ya tsara ganawa da tsohon Minista David Gauke, daya daga cikin masu adawa da ficewar kasar a ranar 31 ga watan gobe ba tare da yarjejniyar ba, ya yi barazanar korar duk wani da ya bijire wa batun na Bredit.

Firayi Ministan ya kuma kira wani taron ministoci a ranar Litinin mai zuwa, dangane da kiran a sake zaben ’yan majalisar muddin suka bijire wa matsayin gwamnatinsa kan ficewar.

Su ma a nasu bangaren shugabannin jam’iyyar da ke mulki a Birtaniyar sun ce duk wani dan majalisar da ya bijire wa bukatar ficewar ba tare da yarjejeniya ba, yana iya rasa damar takara a jam’iyyar a babban zabe na gaba da ma fita daga jam’iyyar kwata-kwata.

Wannan na zuwa ne bayan mako shida kacal da hawa karagar mulki da Mista Borris Johnson ya yi.

Mista Boris Johnson ya yi barazanar cewa ’yan majalisa na jam’iyyarsa da suka bijire wa shirin nasa za su fuskanci kora daga jam’iyyar, yayin da wani dan majalisa, Philip Lee daga Jam’iyyar Conserbatibe ya canja sheka zuwa Jam’iyyar Liberal Democrats mai adawa da ficewa daga Tarayyar Turai, lamarin da ya sa yanzu Johnson ya rasa rinjaye a majalisar gabanin kuri’ar jinkirta ficewa a ranar 31 ga Oktoba.

Bayan wannan kayen da ya sha, Johnson ya ce ba ya da abin da ya rage sai kiran sabon zabe.

A nata bangaren, Tarayyar Turai ta ce Birtaniya na iya ficewa daga Turai ba tare da yarjejeniya ba. EU ta ce Birtaniya ba ta yi wani tayi mai armashi ba game da sake duba yarjejeiyar ficewarta daga kungiyar, kuma a halin da ake ciki, tabbas ana iya rabuwa ba tare da an cimma yarjejeniya ba.

Wannan bayani daga Kungiyar Tarayyar Turai na zuwa ne a daidai lokacin da Firayi Minista Boris Johnson ke yin tsayuwar gwamen jaki a kokarinsa na ficewa da Birtaniya daga Kungiyar Turai koda yarjejeniya ko akasin haka a ranar 31 ga Oktoba mai zuwa, yayin da su kuma ’yan Majalisar Birtaniyan ke kokarin taka masa birki.

Mai magana da yawun Hukumar Tarayyar Turai, Mina Andreeba, ta ce hukumar ta kaddara cewa Birtaniya za ta fice daga Tarayyar Turai a ranar 31 ga  Oktoba kuma a kan haka take aiki.  Ko da aka tambaye ta ko Birtaniya za ta fice babu yarjejeniya? Sai ta ce akwai yiwuwar haka ainun.

Firayi Minista Johnson dai na ci gaba da kekasa kasa cewa ko ta halin kaka sai ya jaddada kuri’ar da al’ummar Birtaniya suka kada a zaben raba-gardama kan ficewa daga Tarayyar Turai a shekarar 2016, inda ya yi barazanar korar duk dan majalisar jam’iyyarsa ta Conserbatibe mai mulki da ya goyi bayan jinkirta ficewar a kuri’ar da aka kada.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin