✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Brexit: Ta ci ba ta ci ba game da ficewar Birtaniya daga EU

Firayi Ministan Birtaniya, Boris Johnson ya bukaci ’yan Majalisar Dokokin kasar su goyi bayan yarjejeniyarsa ta ficewa daga Tarayyar Turai a wani yunkuri na karshe…

Firayi Ministan Birtaniya, Boris Johnson ya bukaci ’yan Majalisar Dokokin kasar su goyi bayan yarjejeniyarsa ta ficewa daga Tarayyar Turai a wani yunkuri na karshe na neman lallai Birtaniya ta fice daga hadakar Turai cikin kwana 6 masu zuwa.

’Yan majalisar za su kada kuri’a game da yarjejejniyar da Johnson ya cimma da EU, kuma idan suka amince da ita, to za a bukaci su amince da jadawalin kwana uku don sake nazartar dokokin ficewar.

Sai dai ka’idar kwana uku na bitar yarjejeniyar ta jawo bacin rai matuka daga bangaren masu hamayya a zauren majalisar.

Mista Johnson, ya gaya wa ’yan majalisar cewa mara bayan ficewar na nufin bai wa kasar damar ficewa kuma ta samu sukunin ci gaba.

’Yan majalisar dai za su fara kada kuri’a kan kudirin yarjejeniyar ficewar, wanda aka wallafa a ranar Litinin.

Zai kira zaben gama-gari

Fadar gwamnatin Birtaniya ta ce, Mista  Johnson zai gabatar da bukatar gudanar da zaben gama-gari muddin Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da tsawaita jinkirin ficewar kasar daga EU har zuwa watan Janairun badi.

A ranar Talata ce, Johnson ya dakatar da kudirinsa na Brexit bayan ’yan majalisar kasar sun yi watsi da shirinsa na ganin an sanya hannu kan kudirin cikin kwana uku domin samun damar ficewa a ranar 31 ga wannan wata na Oktoba.

A halin yanzu, shugabannin  kungiyar kasashen Turai za su yi nazari game da yiwuwar kara wa Birtaniya wa’adin ficewa da kuma tsawon lokacin da hakan zai dauka.

Wasikar da doka ta tilasta wa Mista Johnson aike wa Kungiyar EU bayan ya gaza samun goyon bayan da yake bukata, ta bukaci kara wa’adin ficewar kasar da wata uku nan gaba.

A yanzu dai, fadar Dowing Street na duba yiwuwar kiran zaben gama-gari.

Koda yake dole ne Majalisar Dokokin Kasar ta amince da matakin gudanar da zaben, amma a can baya, ’yan adawa da ke majalisar sun bayyana niyyarsu ta kin amincewa da zaben har sai an yi watsi da batun ficewar Birtaniya ba tare da cimma yarjejeniya ba.

EU na duba yiwuwar sake kara wa Birtaniya wa’adi

Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai sun ce suna duba bukatar da Firayi Ministan Birtaniya Boris Johnson ya sake shigarwa gabansu na tsawaita wa kasar lokacin ficewa daga Tarayyar Turai, bukatar da ’yan majalisar kasar suka tursasa masa mikawa bayan zama na musamman kan sabuwar yarjejeniyar da ya yi nasarar cimmawa da Kungiyar EU.

Yayin zaman majalisar  wakilan majalisar sun ki amincewa da mara baya ga sabuwar yarjejeniyar Johnson matakin da ya kalubalanci kudirinsa na ganin lallai kasar ta kammala ficewa nan da ranar 31 ga watan nan.

Maimakon amincewa da sabuwar yarjejeniyar ta Johnson Majalisar Birtaniya ta kada kuri’ar samar da wani kudiri wanda ya bukaci shugaban ya nemar wa kasar karin wa’adin ficewa maimakon 31 ga Oktoba.

Shugaban na Jam’iyyar Conserbatibe, Boris Johnson wanda a baya ya kafe kan lallai kasar ta kammala ficewa daga EU koda babu yarjejeniya a karshen wannan wata, tuni ya aikewa EU wata wasikar gaggawa da ke neman karin wa’adin wata 3 gabanin ficewar ko da dai bai sanya wa wasikar hannu ba.

Cikin wasikar Johnson ya ja hankali kan illar da sake tsawaita wa’adin kan ficewar Birtaniya zai haifar wa kasar da sauran kawayenta na kasashen Tarayyar Turai.

 EU za ta bai wa Birtaniya lokacin nazari

Shugaban Hukumar Zartarwar Tarayyar Turai Donald Tusk ya bukaci a bai wa Majalisar Dokokin Birtaniya damar nazari da kuma bayyana matsayinta kan yarjejeniyar da Firayi Minista Johnson ya cimma da kungiyar.

Tusk ya bukaci shugabannin Kungiyar EU su amince da dage ranar raba-gari da Birtaniya domin bai wa ’yan Majalisar Dokokin Birtaniya damar nazari da bayyana matsayinsu kan sabuwar yarjejeniyar da Boris Johnson ya cimma da Kungiyar Tarayyar Turai.

Ya bayyana wannan bukata tasa ce a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce yana ba da shawarar Kungiyar EU ta amince da matakin dage ranar raba-garin a rubuce kawai ba tare da an sake kiran wani taron koli a kan batun ba.

Kamfanin Dillancin Larabai na AFP ya ruwaito wata majiyar diflomasiyya mai tushe ta Turai na cewa jakadun kasashen EU za su gudanar da wani taro a wannan makon mai karewa.

Sai dai taron nasu ba na yanke hukunci ba ne, illa kawai na neman jin ra’ayin illahirin kasashen kungiyar ce kan ko akwai bukatar daga wa’adin na Bredit ko kuma babu. Majalisar Dokokin Birtaniya ta amince bisa manufa da sabuwar yarjejeniyar da Firayi Minista Boris Johnson ya cimma da shugabannin EU kan batun.

Sai dai sun yi watsi da bukatar gwamnati na ganin majalisar ta bayyana matsayinta ga yarjejeniyar zuwa yammacin jiya Alhamis, wa’adin da suka ce  ba zai wadatar ba ga nazarin yarjejeniyar wacce ke kunshe a cikin shafuka 110.