✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bruno Fernandes ya amince ya koma Manchester United

Dan wasan Portugal da kungiyar Sporting CP, Bruno Fernandes ya amince da tayin Manchester United. Dan wasan ya amince zai koma Man U a kan…

Dan wasan Portugal da kungiyar Sporting CP, Bruno Fernandes ya amince da tayin Manchester United.

Dan wasan ya amince zai koma Man U a kan kudi Fam miliyan 55.

Yanzu saura yarjejeniya a kan abubuwan da suka shafi dan wasan da duba lafiyarsa.

Aminiya Fernandes a matsayin daya daga cikin manyan batutuwan da suka dabaibaye kasuwancin ’yan wasan Janairun bana, inda Manchester United ta dage kai da fata kan sayan dan wasan, wanda suke ganin zai magance musu matsalolin da suke fuskanta a tsakiya.