✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buda baki ya yi sanadiyyar kashe dadaddar gaba -Shah Rukh Khan da Salman sun sulhunta da juna

A Litinin da ta gabata ce wani abin tarihi ya faru a birnin Mumbai na Indiya, inda shahararrun ’yan fim, Shah Rukh Khan da Salman…

Daga hagu, Salman Khan, Shah Rukh Khan da kuma Baba Siddikui, yayin da jaruman biyu suka sulhuntaA Litinin da ta gabata ce wani abin tarihi ya faru a birnin Mumbai na Indiya, inda shahararrun ’yan fim, Shah Rukh Khan da Salman Khan suka kawo karshen dadaddar gabarsu ta shekara biyar, suka sulhunta da juna. Al’amarin ya faru ne a wani kayataccen otel, inda hamshakin dan kasuwa, Baba Siddikui, ya shirya kwarya-kwaryar buda baki kuma ya gayyaci fitattun ’yan fim da ’yan siyasa da kuma hamshakan ’yan kasuwa.
Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, ’yan fim din biyu, ko a ranar Lahadin da ta gabata, sai da suka hadu a wani gidan shirya fina-finai, amma babu wanda ya kula daya, haka suka wuce juna abinsu.
Tun da farko, Salman Khan ne ya fara isa otel din da misalin karfe 6:30 na yamma, inda ya zauna tare da abokansa, ana jiran cikar lokacin buda baki. Shi kuwa Shah rukh Khan, ya je wurin ne da karfe 7:30 kuma ya zauna a wani teburi da ke kusa da inda Salman ke zaune.
Kamar yadda wata majiya ta shaida al’amarin: “Baba Siddikui ne ya je ya yi magana da Salman, sannan kuma ya je ya gana da Shah Rukh, daga bisani kuma ya tara su wuri daya. A lokacin da suka gana fuska-da-fuska da juna, sai ’yan fim din suka dan canza fuskoki; daga nan kuma suka gaisa hannu-da-hannu kuma suka sumbaci juna.”
Bayan an kammala buda bakin, sai Salman Khan ya kama hanyarsa zuwa aikin daukar fim mai suna ‘Big Boss Season 6,’ a yayin da shi kuma Shah Rukh ya ci gaba da zama tare da mahaifin Salman, wato Salim Khan, har aka kammala buda bakin gaba daya.
Kamar yadda tarihi ya nuna, gaba tsakanin ’yan fim din biyu, ta faro ne tun a 2003, inda Salman ya ziyarci wajen daukar fim din Shah Rukh, ‘Chalte-Chalte’ da nufin ganawa da Aishwarya Rai. A 2004 sun hadu a yayin baikon Farah Khan.
Haka kuma, a 2008, wani sabanin ya shiga tsakaninsu a yayin maulidin Katrina Kaif kuma tun daga lokacin ba su kara musabaha da juna ba, sai fa a wannan rana da suka yi buda baki tare.
daya daga cikin hamshakan ’yan kasuwar da suka halarci dabdalar buda bakin, Shadaab Patel, wanda kuma aboki ne ga attajirin da ya shirya taron, wanda kuma aboki ne har ila yau ga Salman da Shah Rukh, ya bayyana farin cikinsa da wannan sulhu, inda ya ce: “Na yi matukar farin ciki da abokan nan nawa suka hadu kuma suka sulhunta da juna. A lokacin da suka hadu, sun dan canja fuska, amma daga bisani sai suka gaisa kuma suka sumbaci juna. Ina rokon Allah Ya sa su ci gaba da ganawa da juna kuma su mance da duk wani sabani da ya faru tsakaninsu.”