✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budaddiyar wasika zuwa ga amaryata

Gaisuwa mai tarin yawa tare da fatar kina cikin koshin lafiya! Yaya aka ji da dawainiyar shirye-shiryen bikinmu mai alfarma da dimbin tarihi a cikin…

Gaisuwa mai tarin yawa tare da fatar kina cikin koshin lafiya!

Yaya aka ji da dawainiyar shirye-shiryen bikinmu mai alfarma da dimbin tarihi a cikin zukatanmu da kuma zukatan masoyanmu? Allah Ya sa komai yana tafiya yadda kike bukatarsa. Ina fatar Baba da Inna suna lafiya.

Ya ke wannan amarya mai dimbin farin jini da tarin albarka! Na san za ki yi mamakin ganin wannan takarda a daidai wannan lokaci, to ba komai ba ne, ina so ne kawai in yi amfani da wannan dama domin kara tunatar da ke abin da kika riga kika sani. Saboda ke mai ilimi ce da cikakken hankali. Godiya ta tabbata ga Allah da Ya ba ni ke.

Ki sani, ban nemi aurenki ba har sai da na tabbatar da cewa, ke mai tsoron Allah ce, kuma mai kokari wajen bin dokokin shari’a. Saboda haka na san ban zabi wadda ba ita ake nufi ba. Wannan kuma ba shi yake nufin na manta da tsabar kyan halittar da Allah Ya halicce ki da ita ba, ba kuma shi ke nufin na manta da nasabar gidanku da arzikin da kuke da shi ba! Sai dai, ba su ne gabana ba idan aka kwatanta da babban makasudin da ya sa na nemi aurenki.

Manzo Mai tsira da Aminci ne ya ba ni shawara da kansa a cikin lamarin neman auren nan, ashe ko tunda na bi shawararsa, ba ni da sauran wani tsoro. Na san na gama dacewa. Yanzu kin ga auren Ladidi da Illo, ya samu cikas ne sanadiyar zabin kansa da ya bi a wajen yin sa. Domin ya auri Ladidi ce saboda wasu ababe daban, wadanda a lokacin da Manzon Rahama ke ba mu shawara, shi bai dauki shawarar ba, sai ya bi kyal-kyali da wata maslahar ta daban.

Allah Ya ja zamaninki. Duk fadin duniyar nan da kewayenta idan tana da shi, ki sani babu wata wadda nake gani a gabana face ke! Babu wata ’ya mace da nake yi wa fatar alheri kamar ke. Saboda wannan dalili, nake son in sanar da ke wasu ababe da za ki kiyaye min da su idan Allah Ya kawo ki gidana, wadanda kiyaye su ne zai kara ba ni damar kula da hakkokinki da Allah Ya dora min. Kuma in samu cikakkar damar kyautata miki fiye da tunaninki.

Na farko dai, ki kara kaimi wajen bautar Allah da kuma yin da’a ga Ma’aikinSa Annabi Muhammad (SAW). Abu na biyu kuma, ki mutunta ni tare da daukacin ’yan uwana, musamman ma mahaifiyata. Idan kin yi wannan, lallai kin gama yi min komai. Dama can, tun ranar da kika amince da ni a matsayin abokin rayuwa, kin yi min komai.

Ki yi min alkawarin cewa ba zan kai ruwa rana da ke ba a cikin abin da ya shafi ibadar Allah. A duk lokacin Sallah idan ya yi, in ga kin sa kaimi wajen yin ta. Ki lizimci karatun Alkur’ani Mai girma a cikin gidana, kuma ki mayar da hankali a kan karatun da zan ci gaba da  koyar da ke na littattafan addinin Musulunci.

’Yan uwana dukansu ’yan uwanki ne. Mahaifiyata kuma mahaifiyarki ce. Kamar yadda Allah Ya sa a haka nake daukar mahaifanki da ’yan uwanki! To ba dominsu ba, da ba ki samu tarbiyyar da ta ja hankalina zuwa ga aurenki ba! Ba domin wadannan mahaifan naki masu albarka sun haifa ba, da ni ban samu ba. Da ba su ba ni ke ba, da ba a yi maganar aurena da ke ba.

Saboda wannan dalilin ma, na samu zama da mahaifiyata wadda take matukar sonki da kaunarki, mun tattauna a kan yadda zamanku zai kasance idan Allah Ya nufe ki da zuwa gidana. Mahifiyata tana da hakuri, kuma na tabbatar za ta ba ki uzuri a duk inda kika samu kuskure a cikin hakkokinta. Kuma za ta taimaka miki a duk inda bukatar hakan ta taso. To ke ma ina neman ki yi mata uzuri a duk inda ta shiga naki hakkin.

Ni kuma na yi miki alkawarin cewa duk abin da kike so a wurina, zan yi miki shi ba tare da bata lokaci ba, in dai bai fi karfina ko ya saba wa shari’a ba. Idan ban yi miki ba wa zan yi wa? Ke din nan fa, ke ce Allah Ya dauke nauyinki daga kan kowa ya dora a kaina. Kuma wajibin kowane Musulmi ne sauke nauyin da Allah Ya dora masa.

Ya ke amaryata! Zan kasance kusa da ke a duk lokacin da kike bukatar haka, zan share hawayenki in haskaka zuciyarki! Ba zan bari komai ya cutar da ke ba wallahi, matukar ina da iko a kan haka. Shirye nake da in kare mutuncinki da martabarki. Rayuwata fansa ce ga rayuwarki.

Daga karshe ina son ki isar min da godiyata ga mahaifanmu masu albarka. Ki gaya musu ina godiya a kan karimcinsu a gare ni. Kuma ba zan manta da su ba har abada. Har ila yau, ki gaya wa kawayenki, ina yi musu godiya da fatar alheri. Allah Ya ba su maza nagari. Kuma ki hore su da amfani da duk abin da na gaya miki a cikin wannan takarda idan lokacin aurensu ya zo.

Har zan rufe, na manta ban gaya miki sakon gaisuwar abokaina ba, wadanda a gabansu nake rubuta miki wannan takarda, wadanda tuni sun dauki alkawarin bin wannan hanyar da na bi, domin samun zaman lafiya da nasu matan. Gaisuwar ban girma da jinjina a gare ki ya ke sarauniyar ’yan mata! ’Yar autar IYAYEN GIJI (mata), ma’abuciyar hankali da tattausan lafazi da tsoron Allah! Ki huta lafiya.

Daga Nasir Abbas Babi

08033186727