Da Dumi Dumi

Budurwa ta yi hayar tasi 900 don gabatar da bukatar aure ga saurayinta

“Zhang Jianfeng, ina son aurenka, za ka fitowa gaba gadi ka aureni?” wannan sakon soyayya an baje shi ne a birnin Kudu maso gabashin kasar Sin, yayin da wata budurwa ta aike da shi a kan tasi-tasi har 900 da ta yiwo hayarsu don nuna wa saurayinta tana bukatar aurensa.

A ranar 16 ga Maris din bana, budurwar ta kasha Yuan dubu 10 (Dala dubu da 450) don tallata soyayyarta da bukatar aure ga saurayinta a tasi-tasi 900, wadanda suka yi zarya a tsakanin karfe 5 na zuwa 7 na yamma a birnin Zhoushan.

Mista Yuan shi ne manajan kamfanin tallace-tallace, wanda ya baza wannan talla a kan fitilun masu walwali a saman tasi-tasi a birnin Zhousan, inda cewarsa yarinyar tana aiki ne garin Ningbo, saurayinta kuwa yana aiki a Zhoushan. Sun hadu ne da juna a garin Zhuhai. Don haka suka je wajen shakatawa, inda suka kunna kyandura. “A shiorye nike in aureka, ko ka shirya aurena?” inji yarinyar. Shi kuwa saurayin ya mayar da amsar cewa: “Ina son  aurenki. Don Allah ki aureni!”

Wannan ba shi ne karon farko da aka tallata soyayyar bukatar aure a saman fitilun tasi a birnin ba. Sai wannan sakon ya bambanta da sauran, domin wanda aka taba gabatarwa a ranar 25 ga Yunin bana an  yi ta yawo da shi har tsawon kwana 10.

ADVERTISEMENT

A ’yan kwanakin nan matasan masoya sukan fito kai tsaye su bayyana soyayyarsu a kasar Sin. Kuma dimbin matasan masoyan na amfani da kafofin sadarwar zamani don bayana abin da ke cikin zuciyarsu, har ma da gabatar da bukatar aure.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya