Search
Subscribe
Budurwa ta yi yunkurin kashe kanta saboda soyayyar saurayinta 

Budurwa ta yi yunkurin kashe kanta saboda soyayyar saurayinta 

Wata budurwa mai shekaru 17, mai suna Aisha da ke zaune a garin Albarkawa, a garin Gusau ta Jihar Zamfara, ta cinnawa kanta wuta sakamakon saurayinta ya gaza aurenta saboda rashin kudi duk da kaunar da take yi mashi.

Wani makwacin su Aisha ya bayyanawa majiyar mu cewa, yarinyar ta yanke shawarar kashe kanta ne bayan da ta gano saurayin nata, wanda suka dade suna soyayya bashi da kudin da zai iya biyan sadakin aurenta.

Ya ce, tun farko iyayen Aisha sun bukaci saurayin nata, mai suna Umar da ya kawo sadakin aure Naira dubu 17 domin asa rana, sai ya ce ba shi da kudi.

“Ta dauki galan wanda ya ke cike da man fetur ta zuba a jikinta, sannan ta cinnawa kanta wuta da ashana inda nan take wuta takama. Tun kafin ta cinnawa kanta wuta kanwarta tayi kokarin hanata amma taki.

“Daganan sai kawar tafita waje tana neman taimako, wanda wani matashi ya shigo ya kashe wutar da ke ci a jikinta.” In ji shi.

Majiyarmu ta gano cewar an yi wa Aisha maganin gargajiya, sakamakon mahaifinta ya ce ba shi da kudin da zai kaita asibiti.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya ce har yanzu hukumar bata samu labarin faruwar al’amarin ba, amma ya yi alkawarin sanar da mu da zarar hakan ta faru.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin