✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwar soja ta sa sojoji sun kashe mutum 2 a Sakkwato

A ranar Lahadin da ta gabata ce wadansu sojojin sama suka yi harbe wani saurayi da wata mata mai ’ya’ya bakwai lokacin da suka yi…

A ranar Lahadin da ta gabata ce wadansu sojojin sama suka yi harbe wani saurayi da wata mata mai ’ya’ya bakwai lokacin da suka yi hatsaniya da  wadansu matasa a Unguwar Maberar Fulani, a birnin Sakkwato. Hatsaniyar ta kaure ne bayan Sallar Isha’i, bayan da wata da ake zargin budurwar wani sojan sama ne ta samu sabani da matasan unguwar, abin inda ta shaida wa saurayinta sojan ya taho da sojojin suka zo don su nuna wa matasan iyakarsu.

Kamar yadda wata majiya da aka yi komai gabanta ta shaida wa Aminiya, lamarin ya koma fada tsakanin sojojin da matasan bayan da wani dan sanda ya zo wurin domin ceton kanensa da yake cikin wadanda sojojin ke duka a wurin wani mai shayi. A lokacin da soja ya bugi dan sandan, sojojin sun sha da kyar a wurin. Bayan nan ne suka je suka shirya tare da da dawowa da wadansu ’yan uwansu, inda suka far wa duk wanda suka gani a wurin. Nan suka jikkata mutum shida, suka kashe mutum biyu, Maryam Abdurrahaman mai ’ya’ya bakwai, ’yar shekara 40 da wani matashi Abdulsalam Lawal dan shekara 23.

Ahmad Nasiru mai shekara 20 shi ne babban dan marigayiyar da sojoji suka kashe, kuma  a zantawarsa da wakilinmu a Asibitin Kwararru na Jihar Sakkwato, inda suke jiran a ba su gawar mahaifiyarsu domin yi mata sutura, ya ce ba ya nan lokacin da abin ya faru, amma yana dawowa daga wajen aiki mahaifiyarsa ta kira shi tana fada masa cewa kada ya shigo unguwar, saboda sojoji suna fada da matasan unguwa. Ya ce jim kadan bayan magana da mahaifiyarsa sai kanensa ya kira shi, ya fada masa cewa ya zo an harbe ta.

“Ban bata lokaci ba na samo dan Keke NAPEP, muka zo aka tafi da ita asibiti, bayan an duba ta aka ce za a yi mata fida. Mun isa dakin aikin ne, kafin mu shiga ana yi mana tambayoyi ta rasu. Ta bar mu mu bakwai, maza uku mata hudu, ni ne babba a gidan mahaifinmu, wanda ya dade da rasuwa,” inji Ahmad.

Ya ce, “na roki Allah Ya bi mana hakkinmu gare su. Wannan matsala ce ga kasa, matukar ba a hukunta irin wadannan mutane. Ina rokon hukuma ta yi mana adalci, kada jinin mahaifiyata ya zuba a banza.”

Suleiman Aliyu daya daga cikin mutum shida da sojojin suka jikkata, ya ce bayan ya kammala magana da Dokta Sadik kan lamarin sojojin, ya shiga gida sai ya tsaya yana magana da Malam Usman a wurin mai shayi, sai sojojin suka zo wurin cikin mota Hilud da yawa. “Suka tambaye ni ina mai shayi, na ce ya gudu. Suka ce na san abin da ya faru na ce a’a. A nan ne suka rika bin matasan suna harbin kan mai uwa da wabi, sun kamo wani yaro suka dawo. Da suka zo wurina yaron ya rike ni yana fadin don Allah kada in bari su tafi da shi, in taimake shi. Suna son su sa yaron a mota suka kasa, sai wani soja ya zo yana rike da itace, ya rika bugunmu da shi. Yaron ya ji zafi ya sake ni suka sa shi a mota. Ganin kada su illata ni na gudu don shiga wani gida. Ina hanyar shiga gidan, wani ya harbe ni a kafa, harsashin ya fita ya samu matar gidan. Ni ban san harsashi ne suka harbe ni ba sai da muka zo asibiti. Matar ta rasu, an karya wani; abin ba dadi,” inji Suleiman. Abubakar Aliyu dan shekara 22 da sojojin suka tafi da shi ya ce, “Budurwar da ta zama sillar lamarin a Mabera take amma kuma mafi yawan matasan unguwar suna zarginta da karuwanci.”

Ibrahim Umar, wanda sojojin suka fara mari a wurin mai shayin ya ce da idonsa ya ga yarinyar, wadda ake kira Habiba; ita ce yaran suka yi wa magana kuma ita ta zo da sojojin wurinsu.

Habiba Bandi, wadda mahaifinta shi ne Hakimin Mabera Tsohon Gida da ake zargi da kawo sojojin, saboda an yi mata abin da ba ta ji dadi ba,  a zantawarta da wakilinmu a gidansu ta musanta lamarin. “A lokacin da aka yi fadan ina gidanmu. Raini ne kawai da masu jin haushina suke son lika mini abin da ban yi ba. Duk wanda ya ce ni ce, ina jiransa ya ba ni hujjarsa. Ni kawai zan ce Allah Ya isar min, tun lokacin da abu ya faru ba a ce ni ba sai bayan kwana uku?”

Abdurrazak Aliyu, mai shekara 27 mai shayin da aka yi komai a wurin yin shayinsa, ya ce bai san abin da ya faru ba, kawai sojoji ya ga sun zo suka ce wadansu sun ja wata yarinya da suke tare da ita. Ya ce bai sani ba suka kyale shi suka hukunta wadanda ke wurin. Nan ne aka yi rigima daga nan ya tashi.

Dokta Sadik Muhammad Yabo, wakilin mutanen unguwar ya ce duk matakin da ya kamata su dauka kan lamarin za su dauka don a yi musu adalci. Ya ce wannan cin zarafi da sojojin ke yi musu shi ne na uku. Ya ce za su bi hanyar da ta dace kan lamarin har sai an hukunta masu laifi. “In ma Gwamnatin Jihar Sakkwato da ta ba su gidaje suka zauna za ta canja musu wani wuri ne, domin su daina hantarar mutane za su yi, ba za su bari wannan abin ya tafi haka nan ba. A harbi mace mai ’ya’ya ga al’aura, ba ta ji, ba ta gani ba, a harbi matashi ga ciki sai da hanjinsa suka fito, kamar wadanda suka fito yaki, kawai saboda hatsaniya ta shiga tsakaninsu da matasa. Za mu nema masu hakkinsu musamman wannan da aka raba da ’ya’yanta.”

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Kakakin Sojojin Sama a hedikwatarsu ta 119 da ke titin Kontogora a Sakkwato, inda ya aiko wa wakilinmu sakon cewa ba ya son ganin manema labarai da suka je wurin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, Muhammad Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce ba zai ce komai ba, domin ana bincike.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya ce gwamnati ba za ta bar maganar ba har sai an hukunta masu laifi kuma gwamnatinsa za ta dauki nauyin yara bakwai da aka kashe musu mahaifiya.