✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari A Matsayin Tatsuniya? (1)

A cikin ’yan watannin nan, musamman tunda aka buga kugen siyasa da kuma dundufar kakar zaben bana, tambayoyi da yawa sun yi ta zuwa gare ni,…

A cikin ’yan watannin nan, musamman tunda aka buga kugen siyasa da kuma dundufar kakar zaben bana, tambayoyi da yawa sun yi ta zuwa gare ni, musamman daga dalibai da ’yan uwa da abokan arziki da na aiki da kuma, musamman daga ’ya’yana a cikin gida. Tambayoyi ne mabambata da suke bukatar nazari da natsuwa da kuma kawo hujjoji domin amsa su, don su gamsar da wadanda suka yi su. Sai dai ba tambayoyin da suka fi damuna da tsaya mini a rai, sai irin wadanda ’ya’yana sukan sha yi min game da zaben bana da yadda zai wakana, musamman tsakanin Shugaban Kasa Buhari da sauran ’yan takara na adawa, musamman Alhaji Atiku Abubakar ko kuma tambayar da suke yi min wa za ka zaba a tsakanin Nasir El-Rufa’i da Ashiru Kudan a Jihar Kaduna ko kuma wa zan goya wa baya tsakanin Aminu Masari da  Lado Dan Marke a Jihar Katsina?

Tambayoyi da neman bayanai game matsayata dangane da zaben Buhari da Atiku da El-Rufa’i sun ginu ne bisa irin rawar da musamman iyalina suka ga na taka a lokacin zaben shekarar 2015, da irin fafutikar da muka yi na ganin an canja ko da gora, wanda hakan ya kawo gwamnatin Buhari ta ‘canji’ a bisa karagar mulki. Ba sai na nanata ko zayyana waccan gwagwarmaya da muka yi ba, iyaka in ce, ga iyalina sun ga canji sosai bisa ga irin rawar da nake takawa a halin yanzu, ta ‘ko-in’kula.’ Zan dawo kan wannan batu nan gaba.

Su kuwa tambayoyin da suka shafi wa zan zaba tsakanin Nasir El-Rufa’i da Ashiru Kudan sun tusgo ne bisa mazubi na irin gudunmawar da muka bayar a lokacin wancan zabe na 2015, tare da kare dukan wasu muradai na Jam’iyyar APC bisa matakin SAK, ganin cewa guguwar canji ce ke bugawa a wancan lokaci, wato ‘maso-uwa-ya-so-danta’, domin abin da Buhari ke so, shi yawanci ke rububi a lokacin. Ke nan kuri’ata da ta iyalina da wadansu daga masoyana da wadansu daga sauran al’ummar da muka bi gida-gida da aika sakonni ta Malam Nasiru El-Rufa’i ce, tun da a Kaduna nake zaune!

Batun Jihar Katsina kuwa, daga nesa ne muka rika fafutika tunda ba can muke zaune ba, kuma ba can muke jefa kuri’ar ba, amma an sha daga gwargwado domin a ga lallai Nashuni bai kai ba. An kuma yi hakan ne bisa manufar nan da ta gina kwaryar siyasa da zaben 2019, wato SAK!

Saboda haka abin tu’ajjabi ne a ga ina kaffa-kaffa da hidindimun zaben 2019 da kuma nuna rashin damuwa kan jam’iyyun da ke yin takarar, musamman APC da ta yi ikirarin kawo canji in mun zabe ta da kuma Jam’iyyar PDP da ke neman sake bullowa ko kuma farfadowa daga ‘doguwar suma’. Abu ne da nake bayyanawa a fili a cikin gida da kuma wurin tattaunawa da abokan hira da mabiya harkokin siyasar ko a ofis ko bayan kammala Sallar La’asar a bakin garakanmu ko kuma bayan Sallar  Isha, kafin mu shige gidajenmu a cikin unguwa, balle kuma uwa uba, a fagegen soshiyal midiya irin su fesbuk da nake ta yawan wakar, ‘in dai motar siyasa ce to bana ba ni tura ta, amma kuma ku ba mu ce kada ku tura ba.’ Daga wannan lokaci ne tambayoyin suka shiga kwararowa, ana cewa idan ba zan tura motar ba, to me zan tura keke ko babur, ina kuma zan nufa daga nan? Buharin ne ba na yi ko kuma Jam’iyyar APC? Canjin da aka samu ne bai yi min ba ko kuwa bai isa ba ne, ina neman kari? Shin ko na koma goyon bayan Atiku ne, ni ma na yi ‘wanka da ruwan Dala?’ Shin ko Nasir El-Rufa’i ne ya kauce hanyar da aka biyo tun asali daga baya shi ya sa na ja da baya? Ko kuwa dai Masarin ne bai shura kwallon siyasar da mulkin da kyau ba ne, shi ya jawo nake nesa-nesa da motar siyasar? Wadansu ma tambaya suke wai ko dai an yi min alkwarin wani mukami ne, shi ya sa na yi ruwa-da-tsaki a zaben 2015, amma yanzu da na ji shiru, shi ne nake ta ’yan kame-kame? Ko kuwa dai akwai dalili na daban da kila ni kadai na san da shi? Lallai akwai!

To amma ba haka nan sakayau zan bayyana nawa dalilin ko dalilan ba, sai an yi shimfida tukun, kila bayan an nade tabarmar sai mu ga inda batun ya kasance. Ba sai na fada ba, duk wanda ke zaune a doron kasar nan, yana kuma bibiye da yadda motar siyasar ke jirgawa ya san cewa jiya, wato 2015 ba ta yi kama da yau ba, wato 2019. Jam’iyyun dai su ne, duk da an samu karin wasu. Sarakan da ke cikin jam’iyyun da dogarawa da talakawa da ke cikinsu, su ne dai, ba canjawa suka yi ba. Mu ’yan kallon, mu ne dai, sai walankeluwa da muka rika yi wa juna. Abin da kurum ya canja a wannan darar shi ne ba Shugaba Jonathan a wannan zubin, kuma da yake Kartagi irinsa a fagen lale kati ba karami ne ba, dole fasalin jan motar siyasar bana ya canja, duk da ba shi ne babban dalilin sabarta-matin da muke gani ba a yau, mene ne dalili? Ina jin zamowa tatsuniya irin ta Hausawa da Buhari da Nasiru El-Rufa’i da Masari suka yi a tsawon shekara uku da rabi da suka wuce, yana daga cikin dalilan!

Za mu ci gaba