✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari bai yi wa Arewa komai ba – Bafarawa

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dangane da salon mulkinsa musamman rawar da yake takawa ga Arewa.…

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dangane da salon mulkinsa musamman rawar da yake takawa ga Arewa.

A hirarsa da BBC, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana rashin tsaro a matsayin babbar matsalar da kasar ke fuskanta, inda ya bayyana matsalar garkuwa da mutane don karbar kudin fansa a matsayin abin da ya ki ci, ya ki cinyewa.

Ya ce bai ga wani ci gaba da aka samu ba a kasar nan, inda ya ce gara gwamnatin baya da ta yanzu.

Bafarawa ya bayyana wa BBC cewa “Ban taba jin Shugaban Kasar ya zauna da gwamnonin Arewa ba, domin tattauna matsaloli da kuma mafitar Arewa.”

Tsohon Gwamnan ya kuma yi zargin cewa ana nuna bangaranci wajen gudanar da ayyukan ci gaba a kasar nan.

Sai ya yi kira ga Shugaba Buhari da “ya bude kunnunwansa domin sauraren shawarwarin da za su iya kawo ci gaba a kasar nan.”

Kalaman na Attahiru Bafarawa suna zuwa ne bayan lashe zabe da Shugaban Najeriyar ya yi karo na biyu.

Tun a baya dai, Shugaban Najeriyar ya bayyana tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma tattalin arziki a matsayin abubuwan da ya sa a gaba domin kawo ci gaba a kasar.

A martanin da Shugaban Muhammadu Buhari ya mayar ga tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa kan salon mulkinsa, ya ce tsohon Gwamnan ba yi masa adalci ba.

Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin Kakakinsa Malam Garba Shehu a hirarsa ta tarho da BBC.

Ya ce, Bafarawa bai yi wa Shugaban adalci ba dangane da kalaman da ya yi, inda ce, “Bafarawa ya je ya tambayayi jama’ar jihohin Kaduna da Adamawa da Borno bisa kokarin da Shugaban Kasar ya yi a harkar tsaro.”

Garba Shehu ya ce “Abubuwan da suke faruwa a hanyar Kaduna da Birnin Gwari da Zamfara da sauran wurare na damun gwamnati, kuma a yanzu haka Shugaban Kasar ya ba sojojin sama da na kasa umarnin zuwa wadannan yankuna domin magance abubuwan da ke damun jama’ar yankunan.”

Kan batun zargin da Bafarawa ya yi cewa Shugaban bai tattauna da gwamnonin arewa kan ci gaban yankin ba, Malam Garba ya musanta hakan inda ya ce Shugaban yana tattunawa da gwamnoni lokaci bayan lokaci, a wani zubin kuma yakan bi su har jihohinsu domin tattaunawa da su.