✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Atiku namu ne

Salam Edita sai godiya ga ma’aikatan jaridan AMINIYA, saboda ba ku nuna bambanci, kowa naku ne da mai karfi da marar karfi, kowa in ya…

Salam Edita sai godiya ga ma’aikatan jaridan AMINIYA, saboda ba ku nuna bambanci, kowa naku ne da mai karfi da marar karfi, kowa in ya rubuta muku za ku buga masa bukatarsa, haka ake so a yi adalci. Allah Ya taimaka amin. To ga rokona ga al umar Najeriya, musamman ma al’ummar Arewa. Kudancin u kabilun Kudu, sun mika mana, to kada mu ji kunya, an danka mana mulki da Buhari da Atiku namu ne, kada mu yi abin da za a yi mana dariya, Allah Ya zaba mana mafi alheri, Buhari da Atiku, dukansu namu ne, su kuma su tausaya mana su lura da bukatunmu.

Daga Ibrahim Kankoli Jada Adamawa, 07034542318