✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Atiku sun ja daga

Duk da cewa jadawalin shirye-shirye da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar ya nuna cewar jam’iyun siyasa da ’yan takarar neman Shugabancin Kasa da…

Duk da cewa jadawalin shirye-shirye da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta fitar ya nuna cewar jam’iyun siyasa da ’yan takarar neman Shugabancin Kasa da na Majalisun Tarayya za su fara yakin neman zabe a jibi Lahadi, tuni guguwar kamfen ta fara kadawa a dukkan fadin Najeriya.

Hukumar zabe dai ta yi rajista wa jam’iyyu guda 91 ya zuwa wannan lokaci, haka kuma da yawa daga cikinsu sun dau himmar daukar nauyin ’yan takara a matakai da dama, kamar na Shugaban Kasa da kuma ’Yan Majalisar Kasa da kuma na Jihohi.

To, sai dai hankalin jama’ar Najeriya dama masu kula da al’amuran siyasa a fadin duniya ya fi karkata ne a kan manyan jam’iyyu guda biyu, wato jam’iyya mai mulki ta APC da kuma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Tuni dai jam’iyyun biyu sun kammala tarukan fidda gwanayensu a matakai daban-daban, duk da cewa har yanzu akwai yamutsi a wurare da dama.

Babban wajen da jam’iyun guda biyu suka samu nasara shi ne wajen fitar da ’yan takararsu na Shugaban Kasa, a inda ita APC ta sake mika tikitinta ga Shugaba Muhammadu Buhari, shi kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya lashe tikitin PDP, bayan da ya gwabza da ’yan takara har guda goma sha biyu.

Shugaban Hukumar Zabe Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana cewa akwai ’yan takarar Shugaban Kasa guda 79 da za su fafata a zaben na badi, sai dai hakika kallo ya koma ne ga yadda Buhari da Atiku suke kokarin yin wasu abubuwa domin neman kuri’un ’yan Najeriya sama miliyan 80 da za su kada kuri’a a badin.

Bisa ga dukkan alamu dai bana an samu sabon salon kamfen, ganin cewa Buhari da Atiku duk daga yankin Arewa suke, ba kamar abin da ya faru a shekarar 2015 ba, lokacin da Buhari ya fafata da Shugaban Kasa a wancan lokacin, wato Dokta Goodluck Jonthan, wanda ya fito daga yankin Kudu.

A wancan lokacin dai akwai miliyoyin mutane da suka jefa kuri’a saboda yankin da suka fito. Haka kuma addini ya yi tasiri matuka a wancan lokacin amma bisa ga dukkan alamu hakan ba zai faru ba a zaben Shugaban Kasa mai zuwa, ganin cewar Buhari da Atiku dukkanninsu Musulmi ne; don haka dukkannin ’yan takarar sai dai su yi gadara da wasu abubuwa daban.

A wata hira da ya yi da Aminiya, Sanata Abu Ibrahim wanda ke wakiltar Katsina ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa Buhari zai kayar da Atiku a zabe.

Sanatan wanda shi ne shugaban wata kungiya da ake kira National Committee for Buhari Support Groups (NCBSG), ya ce kasancewar Atiku a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP ta fadi gasassa a gare su.

“Hakika ni farin ciki nake yi, domin duk wani ta’adi da tsohon Shugaban Kasa Obasanjo ya aikata tare suka yi da Atiku, kuma ’yan Najeriya ba su manta ba,” inji shi.

Ya kara da cewa yana da yakinin Buhari zai ci zabe koda a yau za a yi, domin ’yan Najeriya sun san cewa shi ba mai son zuciya ba ne kuma ba zai ci amanarsu ba.

To, shi ma Shugaban Jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus ya bayyana cewa suna da yakinin Atiku zai kayar da Buhari. Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara a babban offishin kamfen na jam’iyyar da ke Abuja.

“Tabbas dan takararmu zai kayar da Buhari, domin ’yan Najeriya sun gaji da jam’iyar APC, wacce babu abin da ta kawo sai yunwa da kunci da talauci,” inji shi.

Buhari da Atiku sun ja daga

Hikimar Buhari:

Tuni dai Shugaba Buhari ya sake daukar aniyar zarcewa tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo; wani mataki da masu fashin baki ke ganin ya dace, domin hakan zai sa jama’ar yankin Kudu Maso Yamma (South West) su mara masa baya.

Binciken Aminiya ya nuna cewa Shugaba Buhari da magoya bayansa har yanzu suna da yakinin cewa za su kwashi garabasa a yankunan Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Gabas, sa’annan kuma shi Osinbajo, tare da goyon bayan tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu da sauran ministoci daga yankin Kudu Maso Yamma za su ci nasara, kamar dai yadda ya faru a shekarar 2015.

Duk da masu hangen nesa suna ganin cewa zai samu matsala a wasu yankuna na Kudu, Shugaba Buhari ya samu nasarar kutsawa yankin Kudu Maso Gabasta hanyar samar musu da abubuwan more rayuwa, kamar ci gaba da gina hanyoyi da kuma babbar gadar da ke yankin (Second Niger Bridge).

Sai dai wasu mutane suna ganin wannan ba wani abu ba ne domin jama’ar yankin ba za su taba amincewa da APC ba.

Abu na uku da ake ganin Shugaba Buhari zai yi takama da shi, shi ne yaki da cin hanci da rashawa. Duk da cewa jam’iyyar PDP tana zarginsa da lullube ’yan jam’iyyarta APC, a ’yan kwanakin nan akwai ’yan APC din da ke fama da bincike daga hukumomin tsaro na DSS da EFCC.Tuni dai DSS sun binciki Shugaban Jam’iyyar APC, Kwamared Adams Oshiomhole bisa zarginsa da karbar hanci daga wasu ’yan takara. Haka kuma wata babbar kotu ta dage kariya da ta bai wa tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Uzo Kalu, sa’annan kuma wata hukumar gano ta’annati ta kama dan takarar gwanna a Jihar Imo, Hope Uzodinma.

Sai dai duk da haka jam’iyar adawa ta PDP ba ta yarda ba, a inda Kakinta Kola Ologbondiyan ya ce duk abin da jami’an tsaron suke yi boge ne, domin sun ga lokacin zabe ya karato.

To sai dai wani Kakaki a wata kungiya mai bincike kan al’amuran siyasa (Centre for Democracy and Debelopment), Mista Armsfree Ajanaku ya bayyana cewa abin da ’yan Najeriya suka fi damuwa da shi, shi ne a ci gaba da binciken masu laifuka. Ya kara da cewa idan har ana binciken ’yan jam’iyya mai mulki da kuma ’yan adawa, mutuncin Najeriya zai haskaka a idon duniya.

Hikimar Atiku:

Shi ma dan takarar jam’iyar PDP, Atiku Abubakar ya dauko tsohon Gwamnan Jihar Anambara Mista Peter Obi a matsayin mataimakinsa.

Masu fashin baki suna ganin shi ma wannan zabi da ya yi ka iya yin tasiri, domin jama’ar yankin Kudu Maso Gabas za su zabe shi sosai ba tare da sun yi la’akari da abubuwan da Shugaba Buhari ya yi musu ba.

Ana ganin kuma jama’ar Kudu Maso Kudu za su zabi Atiku sosai domin daga wancan yankin ne tsohon Shugaba Jonathan ya fito, haka kuma shi ma shugaban jam’iyyar PDP Secondus daga can yake.

To, sai dai ana ganin mutane irin su tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom wato Sanata Godswill Akpabio za su iya taimaka wa Buhari ya sami kashi 25 da yake bukata a kowace jiha domin cin zabe.

Binciken Aminiya ya nuna cewar Atiku dai ya yi kokari wajen amfani da kafafen sada zumunta na zamani irin su Facebook, Twitter, Instagram da sauransu wajen shawo kan matasa. Matasa dai za su taka rawar gani matuka a zabuka masu zuwa. Don haka ana ganin in dai har suka fito kuma suka zabi Atiku za su iya yin illa.

Bayan haka ana ganin kamar jam’iyyar PDP tare da dan takararta za su iya yin amfani da kudi domin cin zabe, kamar dai yadda ake zargin cewa Atiku ya yi amfani da miliyoyin daloli wajan sayen daliget a birnin Fatakwal, abin da ake gani Shugaba Buhari ba zai bari a aikata a jam’iyyarsa ta APC ba; in dai har ya san za a kwashi kudaden al’umma.

“To, ni ina ganin tabbas PDP za su yi wa APC illa ta wannan gefen, domin akwai mutane da dama da ke fama da yunwa ku ma za su iya sayar da kuri’unsu,” inji Mukhtar Ali, wanda shugaban wata kungiyar matasa ne a Kano.

Sa’annan kuma wani abu da Atiku ya yi shi ne, ya yi kokarin jawo dukkannin wadanda suka yi takara da shi a jikinsa, abin da Shugaba Buhari bai yi ba, har ta kai ga mutane irin Sanata Rabiu Kwankwaso suka yi tofin Allah-tsine, suka fice daga APC.

A yanzu haka dai Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki shi ne Shugaban Kwamitocin Kamfen din Atiku. Shi kuma Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato shi ne zai kula da al’amuran zabe a yankin Arewa Maso Kudu; Ibrahim Dankwambo shi ne shugaba a yankin Arewa Maso Gabas, Samuel Ortom shi ne a Arewa ta Tsakiya, Gwamna Dabid Umahi na Jihar Ibonyi shi ne a Kudu Maso Gabas, Nyesom Wike na Jihar Ribas shi ne a Kudu Maso Kudu; sa’annan kuma tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose shi ne zai gudanar da hidimar kamfen a yankin Kudu Maso Yamma.

Ita dai jam’iyyar APC tun da ta nada Ministan Sufuri Rotimi Amaechi a matsayin jagoran kamfen dinta na Shugaban Kasa da kuma Lauya Festus Kiyamo a matsayin Kakaki, har yanzu ba a sake nada kowa ba – abin da ake ganin zai iya yi musu illa a nan gaba.

Mutane irin su Alhaji Ibrahim Jirgi, wanda yana daga cikin Kwamitin Kamfe na dan takarar Shugaban Kasa daga APC a shekarar 2015, ya ce tun da suka tura mota ta tashi, tserewa ta yi ta bar su suna susar keya.