✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Muslim

Babi na dari da Sittin da Shida: Wanda ya ga abokin gaba ya daukaka muryarsa cewa: “Jama’a ku kawo taimako, har sai da ya jiyar…

Babi na dari da Sittin da Shida: Wanda ya ga abokin gaba ya daukaka muryarsa cewa: “Jama’a ku kawo taimako, har sai da ya jiyar da mutane.”:

714. An karbo daga Makkiyu dan Ibrahim ya ce: “Yazid dan Abu Ubaidatu ya ba mu labari daga Salmata cewa: Lallai shi ya ba shi labari ya ce: “Na fita daga Madina ina tafiya ta wajen dajin nan sai da na kai ga Saniyyat (tsauni) ta Algaba (dajin nan) sai yaron Abdurrahman dan Awfu ya hadu da ni na ce: “Me ya same ka? Ya ce: “An kwace taguwar da ke dauke da ruwan Annabi (SAW). Na ce, “Wane ne ya kwace ta? Ya ce, “kabilar Gadafan da Fazarat.” Sai na yi ihu da karfi har sau uku, ina kokarin jiyar da duk wanda ke tsakanin manyan tsaunukan nan biyu. Ina fadin cewa: “Jama’a ku kawo taimako da sauri!” Sannan na hau na bi su har sai da na cim musu (iske) su, suna jan ta. Sai na rika harbinsu ina fadin cewa: Ni ne Salmatu dan Akwa’u, Yau wuni ne na neman taguwar shayarwa. Sai na kwace ta daga gare su kafin su sha daga gare ta. Na koro ta ina jaye da ita, sai Annabi (SAW) ya hadu da ni, na ce: “Ya Manzon Allah! Lallai mutanen nan suna cikin kishirwa, don haka na yi gaggawa a kansu saboda kada su sha daga abin shansu, ka aika da wadansu, su bi sawunsu. Sai (Annabi) ya ce: “Rabu da su, ka ci nasara a kansu, ka yafe musu. Kuma lallai mutane ana zaunar da su bisa ga yadda mutanensu suke.”

Babi na dari da Sittin da Bakwai: Wanda ya ce, “Ku karba, ni ne dan wane, kamar yadda Salmatu ya ce: “Karbe ta ni ne Salmatu dan Akwa’u.”:

715. An karbo daga Ubaidullah ya ce: “Daga Abu Is’hak ya ce, wani mutum ya tambayi Barra’u dan Azib (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Shin ya Abu Amratu! Shin kun gudu a Yakin Hunain? Barra’u ya ce: “Amma Manzon Allah (SAW) bai juya baya (gudu) ba a wannan rana. Sufiyan dan Haris ya kasance yana rike da ragamar alfadarinsa. Lokacin da mushirikai suka lullube shi sai ya sauka yana cewa: “Ni ne Annabin ba karya ba ne. Ni ne dan Abdulmudallib.” Ya ce: “Ran nan ba a ga wanda ya fi shi jaruntaka ba.”

Babi na dari da Sittin da Takwas: Idan abokin gaba ya yarda da hukuncin wani mutum:

716. An karbo daga Sulaiman dan Harb ya ce: “Shu’abah ya ba mu labari daga Sa’ad dan Ibrahim daga Abu Usamatu dan Sahlu dan Hunaif daga Abu Sa’idul Khuduri (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Lokacin da kabilar Bani kuraiza suka yarda da sulhu bisa hukuncin Sa’ad. Sai Manzon Allah (SAW) ya aika aka zo da shi yana bisa wani jaki saboda ya kasance kusa da shi. Lokacin da ya kusanto sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku tashi zuwa ga shugabanku! Ya zo ya zauna kusa da Manzon Allah (SAW) ya ce masa: “Lallai wadannan sun yarda da sulhu bisa hukuncinka. Sai ya ce: “Lallai ni, zan yi hukunci da a kashe dukan mayakansu kuma a daure zuriyarsu bisa bayi.” Sai (Annabi) ya ce: “Lallai ka yi hukunci a tsakaninsu da  irin hukuncin Allah.”          

Babi na dari da Sittin da Tara: Hukunci kashe fursunan yakin da wanda ke tsare da wani abu:

717. An karbo daga Isma’il ya ce: “Malik ya ba mu labari daga dan Shihab daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya shigo a ranar da aka ci Makka da yaki yana sanye da malfar yaki. Lokacin da ya tube sai wani mutum ya zo ya ce: “Lallai ga dan Akdal can yana rataye (rungume) da suturar Ka’aba.” Sai ya ce: “Ku kashe shi.”