✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Dari da Tamanin da Biyar: Wanda ya samu rinjaye a kan abokan gabansa sa’an nan ya…

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Dari da Tamanin da Biyar:

Wanda ya samu rinjaye a kan abokan gabansa sa’an nan ya kwana nan gari har kwana uku.

19. An karbo daga Muhammad dan Hatim ya ce: “Rauhu dan Ubadatu ya ba mu labari ya ce, Sa’ad ya ba mu labari daga Kattada ya ce, “Anas dan Malik ya ambata mana daga Abu Dalhat (Allah Ya yarda da su) daga Annabi (SAW) cewa: “Lallai shi ya kasance idan ya samu nasara a kan abokan gaba, yakan zauna a farfajiyar gari kamar kwana (dare) uku.”

 

Babi na Dari da Tamanin da Shida:

Wanda ya raba ganimarsa ta yaki ko a bisa ga hanya (komowarsa) daga tafiya. Rafi’u ya ce: “Mun kasance tare da Manzon Allah (SAW) lokacin da muka iso Zul Hulaifa, mun samo taguwa da tumaki, kuma ya daidaita tumaki goma bisa rakumi daya.”

20. An karbo daga Hudabat dan Khalid ya ce: “Hammam ya ba mu labari daga Kattada cewa: “Lallai Anas ya ba shi labari ya ce: “Annabi (SAW) ya yi Umara daga Ji’ranata inda ya raba ganimar yakin Hunain.”

 

Babi na Dari da Tamanin da Bakwai:

Idan kafiri ya samu ganimar dukiyar Musulmi sa’an nan shi (Musulmi) ya iske ta. Dan Numair ya ce: “Ubaidullahi ya ba mu labari daga Nafi’u daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Doki ya taba gudu masa, sai abokin gaba ya kama shi. Ana nan haka Musulmi suka samu nasara a kan kafiran. Sai aka mayar masa a zamanin Manzon Allah (SAW). Kuma bawansa ya taba gudu ya fada hannun Romawa, lokacin da Musulmi suka samu nasara a kansu, Khalid dan Walid ya  mayar masa bayan rasuwar Annabi (SAW).”

 

21. An karbo daga Muhammad dan Basshar ya ce: “Yahaya ya ba mu labari daga Ubaidullahi ya ce, Nafi’u ya ba ni labari cewa: Lallai wani bawan Abdullahi dan Umar ya taba gudu ya fada hannun Romawa. Khalid dan Walid ya samu nasara a kansu, ya mayar da shi ga Abdullahi. Kuma lallai wani dokin Abdullahi dan Umar ya taba gudu ya fada hannun Romawa da aka ci su da yaki aka mayar da shi ga Abdullahi.”

 

22. An karbo daga Ahmad dan Yunus ya ce: “Zuhair ya ba mu labari daga Musa dan Ukba daga Nafi’u daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), cewa: Lallai shi ya ya kasance a bisa wani doki ranar haduwar Musulmi da shugaban Musulmi Khalid dan Walid a wannan yini Abubakar ya aika shi (Khalid). Sai abokin gaba ya karbe shi (doki), da aka ci abokan gaba da yakin, Khalid ya mayar masa da dokin.”

 

Babi na Dari da Tamanin da Takwas:

Wanda ya yi magana da harshen Farisanci ko da wata salon magana na Larabci. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Da sabanin harsunaku da launukanku…” (K:30:23). Da fadarSa cewa: “Ba Mu aiko wani Manzo ba face da harshen mutanensa…” (K:14:4).

 

23. An karbo daga Amru dan Aliyu ya ce: “Abu Asim ya ba mu labari ya ce, Hanzalatu dan Abu Sufiyan ya ba mu labari ya ce, Sa’id dan Mina’u ya ce: “Jabir dan Abdullahi (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na ce, Ya Manzon Allah! Mun yanka wata tinkiyarmu kuma na gasa garin sha’ir sa’i daya. Ka zo da jama’arka mu ci, sai Annabi (SAW) ya daukaka muryansa ya ce: “Ya ku masu hakar Khandak (gwalalo)! Ku zo, Jabir dan Abdullahi ya girka mana Su’r.” (kalmar Su’r da harshen Farisanci shi ne abinci).”

 

24. An karbo daga Habban dan Musa ya ce: “Abdullahi ya ba mu labari daga Khalid dan Sa’id daga babansa daga Ummu Khalid ’yar Khalid dan Sa’id ta ce: “Na tafi ga Manzon Allah (SAW) tare da babana lokacin ina sanye da wata taguwa fatsa-fatsa. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Sanah! Sanah!” Abdullahi ya ce: “Kalmar (mutanen) Habasha ce, ma’anar ya yi kyau.” Ta ce, “Sai na tafi bayansa ina wasa da hatimin Annabci, babana ya hane ni. Manzon Allah (SAW) ya ce, “kyale ta.” Sa’an nan Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ki sanya ta har sai ta rududdege, ki sanya ta har sai ta rududduge, ki sanya ta har sai ta rududduge (mutu).” Abdullahi ya ce: “Ta rika sanya taguwar nan kuma ta yi karko har ta kode ta zamo baka, (saboda addu’ar Annabi).”