✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari Da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Goma Sha Uku: Albarkar dukiyar yakin daukaka kalmar Allah mai shi (mai yi) yana raye ko…

Tare da Sheikh Yunus Is’hak

Almashgool, Bauchi

Babi na Goma Sha Uku: Albarkar dukiyar yakin daukaka kalmar Allah mai shi (mai yi) yana raye ko yana mace tare da Annabi (SAW) ko da mai shugabantar al’amura:

77. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Na ce da Abu Usamatu shin Hisham dan Urwatu ya ba ku labari daga babansa daga Abdullahi dan Zubair ya ce: “Lokacin da Zubair ya tsaya a ranar Yakin Jamal. Ya kira ni na tsaya a gefensa sai ya ce: “Ya dan dana! Lallai ka sani yau babu wanda za a yaka face azzalumi ne ko wanda aka zalunta. Kuma ban ganin kaina face ina daga cikin wadanda za a kashe bisa zalunci. Kuma lallai mafi girman nufina, shin kana ganin ko idan muka biya bashin da ke kaina dukiyarmu za ta saura kuwa? Sai ya ce: “Ya dan dana! Ka sayar da kayanmu ka biya mini bashi. Kuma ya yi wasiyya da daya cikin uku na dukiyar, daya cikin uku ga dansa Abdullahi dan Zubair, yana cewa: Daya cikin ukun uku. Kuma dukan abin da  ya rage dai a ba da daya cikin ukun uku, ga ’ya’yanka. Hisham ya ce: “Kuma wadansu daga cikin ’ya’yan Abdullahi sun gama auna sashen yawan ’ya’yan Zubair kamar Khubaib da Abbad saboda shi a wannan rana yana da yara maza tara da ’ya’ya mata tara. Abdullahi ya ce: “Sai ya rika yin mini wasiyya da biyan bashinsa. Yana cewa: “Ya dan dana! Idan har ka gajiya game da biyan bashin nan ka nemi taimakon waliyyina. Ya ce, “Wallahi ban san wane ne ba har sai da na ce, “Ya Baba! Wane ne waliyyinka? Ya ce: “Allah!” Ya ce: “Wallahi ban taba fadawa cikin bakin ciki irin na wannan bashi ba face na ce, Ya Waliyyin Zubair! Ka biya masa bashinsa. Daga nan sai Allah Ya taimake ni wajen biya. A ran nan dai aka kashe Zubair (Allah Ya yarda da shi), bai bar Zinari daya ko Dirhami ba, face wasu filaye a dawa da gida goma sha daya a Madina. Da gidaje biyu a Basrah da gida daya a Kufah da wani gida a Masar. Ya ce: “Abin da ya sanya bashi ga babana saboda idan mutum ya zo da ajiyar kudinsa sai ya ce: “Ka bar mini bashinsa saboda ina jin tsoron halakarsu.” Kuma ya ce: “Shi bai taba shugabantar kowa ba kuma bai taba zama mai karbar haraji ba, abin da ya mallaka face sun kasance ta hanyar ganima ne da ake fita yakin daukaka kalmar Allah tare da Manzon Allah (SAW), ko yakin da yayi tare da Abubakar da Umar da Usman (Allah Ya yarda da su).” Abdullahi ya ce: “Saboda haka da na lasaffa abin da  ke kansa na bashi sai na samu kamar miliyan biyu ne da dubu dari biyu.” Sai Hakim dan Hizam ya hadu da Abdullahi dan Zubair ya ce: “Ya dan dan uwana! Nawa ne ke kan dan uwana na bashin? Sai ya boye masa, ya ce: “Dubu dari ne.” sai Hakim ya ce, “Wallahi ban tsammanin dukiyarku zan ta biya wannan bashi.” Sai Abdullahi ya ce: “Yaya za ka yi idan haka aka ce: “Ana bin ka miliyan biyu da dubu dari biyu?” Ya ce: “Ban ganin za ku iya biyan wannan, idan har kun gajiya to, ku nemi taimakawata.” (Abdullahi) ya ce: “Zubair ya sayi gonar Gabah ce da kamar dubu dari da saba’in.” Sai Abdullahi ya sayar da ita bisa farashin miliyan daya da dubu dari shida. Sa’an nan ya mike ya ce: ‘Wanda ke bin Zubair bashi ya zo ya karba a gonarmu ta Gabah.” Sai Abdullahi dan Ja’afar ya zo masa, saboda shi yana bin Zubair dubu dari hudu. Ya ce da Abdullahi idan kuna so sai in bar muku? Abdullahi ya ce: “A’a, in kun so ina yi muku jinkiri zuwa wani lokaci? Abdullahi ya ce: ‘A’a,” Abdullahi ya ce, sai ya ce: “Ku yanka mini wani yanki daga gonar nan.” Sai Abdullahi ya ce: “An b aka daga nan zuwa can.” Da ya sayar sai ga shi ta biya bashinsa. Ya rage rabon mutum hudu da rabi (daga fadin gonar). Sai ya gabata ga Mu’awiyya yana tare da Amru dan Usman da Munzir dan Zubair da Dan Zama’atu. Sai Mu’awiyya ya ce: “Na wane kuka sanya wa Gabah (gonarku) kudin? Ya ce: “Kowane kaso na bisa farashin dubu dari.” Ya ce: “Kaso nawa suka saura? Ya ce, “Kaso hudu da rabi.” Munzir dan Zubair ya ce: “Na dauki rabo guda bisa dubu dari.” Amru dan Usman ya ce: “Na dauki kaso daya bisa dubu dari.” Dan Zama’atu ya ce: “Na dauki kaso daya bisa dubu dari.” Sai Mu’awiyya ya ce: “Nawa ya saura? Ya ce: “Kaso guda daya da rabi.” Ya ce: “Na dauke su bisa dubu dari da hamsin.” Ana nan haka sai Abdullahi dan Ja’afar ya sayar da rabonsa ga Mu’awiyya bisa farsashin dubu dari shida.” Da Abdullahi ya kare biyan wannan bashi. Sai ’ya’yan Zubair suka ce: “To ka raba sauran a tsakaninmu bisa gadonmu.” Ya ce, “A’a, wallahi ba zan raba ba ta a tsakaninku sai na yi shela har lokutan bashinsa ya gabato wato lokacin Hajj da kamar shekara hudu. Ya rika cewa: Duk wanda ke bin Zubair bashi ya zo mu biya shi. Sai ya kasance kowace shekara da ta gabato sai ya rika shela lokacin Hajji da shekara hudu suka shude sai ya raba abin da  ya saura a tsakaninsu.” Kuma Zubair ya kasance yana da mata hudu, ya dauke daya cikin uku (na wasiyya), daga sai da kowace mace ta samu rabon miliyan daya da dubu dari biyu. Kuma dukiyarsa da ya bari da aka lasaffa aka samu miliyan hamsin da dubu dari biyu.” (Wannan ya bayyana mana albarkar dukiyar ganima, koda yake mutane zasu fahimci yadda ya tara wannan bashi mai yawa a kansa don tsoron kada ya ci amanar masu bashi ajiyar dukiyoyinsu Allah Ya sa mu dace).