✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Goma Sha Uku: Albarkar dukiyar yakin daukaka kalmar Allah mai shi (mai yi) yana raye ko…

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Goma Sha Uku: Albarkar dukiyar yakin daukaka kalmar Allah mai shi (mai yi) yana raye ko yana mace tare da Annabi (SAW) ko da mai shugabantar al’amura:

Babi na Goma Sha Hudu: Idan shugaba ya aika da wani dan aike cikin wata bukata ko ya shugabantar da shi da wani matsayi shin za a yi rabo da shi?:

78. An karbo daga Musa ya ce: “Abu Awanatu ya ba mu labari ya ce, Usman dan Mauhib ya ba mu labari daga Dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Abin da  ya tsare Usman (RA) daga Yakin Badar saboda ya kasance ’yar Manzon Allah (SAW) tana aurensa kuma lokacin ta kasance ba ta da lafiya. Sai Annabi (SAW) ya ce masa: “Lallai kai ma kana da sakamakon wanda ya halarci Yakin Badar da rabonsa (na ganima).”

 

Babi na Goma Sha Biyar:

Dalilin sanya daya cikin biyar na ganimar yaki bisa bukatun Musulmi. Haka ya nuna bisa ga abin da kabilar Hawazin suka roka daga Annabi (SAW) bisa ga ya mayar musu da ganimar yakinsu gare su. Saboda shi an shayar da da shi da wani daga cikinsu, sai ya nemi izinin Musulmi. Da bayanin abin da  Annabi (SAW) ya kasance yana alkawari da shi ga mutane cewa: Zai ba su wani abu daga dukiyar fai’u (ganimar da aka samu ba ta hanyar zubar da jini ba). Da karin da yake yi daga daya cikin biyar na ganimar yaki. Da bayanin abin da  ya bayar ga mutanen Madina da kuma magana kan abin da  ya bayar ga Jabir dan Abdullahi daga dabinan Khaibara.

 

79. An karbo daga Sa’id dan Ufair ya ce: “Laisu ya ba mu labari ya ce Ukail ya ba ni labari daga Dan Shihab ya ce: “Urwatu ya ambata cewa, lallai Marwan dan Hakam da Miswar dan Makhramat sun ba shi labari cewa: Lallai Manzon Allah (SAW) ya fada a lokacin da tawagar Hawazin suka zo masa suna masu mika wuya (Musulunta). Sai suka roke shi da ya mayar musu da dukiyarsu da fursunan yakinsu. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce musu, “Mafificiyar magana gare ni ita ce wadda ta fi gaskiya. Wato su zabi daya cikin biyu dukiya ko fursunan yaki. Saboda na yi jinkirin rabon ganimarsu. Kuma hakika Manzon Allah (SAW) ya jira karshensu (al’amarinsu) da kamar kwana goma lokacin da ya tafi Da’ifa. Lokacin da suka fahimci lallai Manzon Allah (SAW) ba zai ba su duka face daya cikin abubuwan nan biyu, sai suka ce: “Lallai mun zabi fursunan yakinmu.” Sai Manzon Allah (SAW) ya mike cikin jama’ar Musulmi ya yabi Allah da abin da Ya dace da Shi. Sa’an nan ya ce: Bayan haka lallai hakika na ga ya kamata in ba su fursunan yakinsu, amma duk wanda yake son ya bar mini rabonsa to ya aikata haka. Kuma duk wanda ke son in ba shi rabonsa zan ba shi bisa ga abin da Allah Ya ba ni fai’u shi yana neman hakkinsa. Sai mutane suka ce, “Ya Manzon Allah! Mun halatta maka, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: Bisa ga haka dai ba za mu fahimci wanda ya bar mana ba da wanda bai bar mana ba. Saboda haka ku tafi ku yi shawari abin da  kuka yanke shawari da malamanku sai su bayyana mana. Sai suka koma  ga manyansu suka yi magana da su. Sa’an nan suka komo ga Manzon Allah (SAW) suka ba shi labari cewa: Lallai su, sun halatta masa kuma sun yi izini.” Wannan shi ne labarin da ya iso gare mu game da fursunan yakin da aka kamo daga Hawazin.