Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

BUHARI DA MUSLIM

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

94. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari ya ce, Zuhuri ya ba mu labari ya ce, Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), cewa: “Lallai wadansu jama’a daga mutanen Madina sun taba cewa da Manzon Allah (SAW) lokacin da Allah Ya bai wa ManzonSa (SAW) dukiyar fai’u daga dukiyar Hawazin. Sai ya rika bayarwa ga wadansu jama’a daga Kuraishawa taguwa dari. Sai suka ce, “Allah Ya gafarta wa Manzon Allah (SAW) yana bayarwa ga Kuraishawa yana barinmu, ga takubbanmu na digar (zubar) jinin abokan gabansu.” Anas (RA) ya ce: “Sai aka bayar da labari ga Manzon Allah (SAW) game da wannan magana tasu, sai ya aike zuwa ga mutanen Madina ya tara bisa wata rumfar fata mai launin ja bai rage kowa ba daga cikinsu. Lokacin da suka taru sai Manzon Allah (SAW) ya zo musu ya ce: “Wane labari ne ya zo mini daga gare ku? Sai malamansu suka ce masa, “Masu ra’ayi (shekaru) daga cikinmu ba su ce komai ba, amma wadansu daga cikinmu masu kananun shekaru su ne suka ce: “Allah Ya gafarta wa Manzon Allah (SAW) yana bayarwa ga Kuraishawa yana barin mutanen Madina. Takubbanmu na digar jinin abokan gabanmu.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Lallai ni, ina bayarwa ne ga sababbin musulunta. Shin ba za ku yarda mutane su tafi da dukiyar ba, ku kuma ku koma da Manzon Allah (SAW) zuwa ga masaukanku ba? Ina rantsuwa da Allah abin da  kuke komawa da shi na alheri, su ba za su koma da kamarsa ba. Sai suka ce, “Gaskiya ce, ya Manzon Allah! Hakika mun yarda.” Sai ya ce musu: “Lallai za ku samu wasu bambance-bambance sosai a bayana, to ku yi hakuri har sai kun hadu da Allah da ManzonSa (SAW) bisa tafkin.” Anas ya ce, “Ba mu yi hakuri ba.”

ADVERTISEMENT

95. An karbo daga Abdul’aziz dan Abdullahi Uwaisiyyu ya ce: “Ibrahim dan Sa’d ya ba mu labari daga Salih daga Dan Shihab ya ce, “Umar dan Muhammad dan Jubair ya ce: “Jubair dan Mud’im ya ba ni labari cewa: Lallai shi wata rana yana tare da Manzon Allah (SAW) da wadansu mutane tare da shi lokacin da suke komowa daga Yakin Hunain. Sai wadansu kauyawa daga Larabawa suka rika nacewa suna rokon Manzon Allah (SAW) har suka ture shi bisa kayar Samura, mayafinsa ya makale. Manzon Allah (SAW) ya tsaya ya ce: “Ku miko mini mayafina, da dai a ce duk wadannan kayoyi za su zama taguwa. Lallai da kuwa na raba su a tsakaninku. Sa’an nan ba za ku same ni marowaci ba, kuma ba za ku same ni makaryaci ba, kuma ba za ku same ni matsoraci ba.”

96. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Is’hak dan Abdullahi daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), ya ce: ‘Na kasance ina tafiya tare da Annabi (SAW) yana sanye da wani mayafi (taguwa) na Najran mai dajiya da kaushi. Sai wani Balaraben kauye ya iske shi ya fizge masa taguwa da tsanani har sai da na ga alamar fizagawar nan a fadin kafadar Annabi (SAW). Dajiyar taguwar ta fito saboda tsananin fizgawarsa (bakauyen). Sa’an nan ya ce: “Ka umarta a ba ni wani abu daga dukiyar Allah da ke tare da kai. Sai (Annabi SAW) ya zuwa juya gare shi ya yi dariya. Sa’an nan ya umurta aka ba shi wata kyauta.”

ADVERTISEMENT

97. An karbo daga Usman dan Abu Shaibah ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga Mansur daga Abu Wa’il daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Lokacin da yinin Yakin Hunain ya kasance Annabi (SAW) ya fifita wadansu da kyauta a wurin rabo. Sai ya bai wa Akra’u dan Habus taguwa dari. Ya bai wa Uyainatu kamar haka. Ya bai wa wadansu manyan Larabawa ya fifita wadansu a wannan rana. Sai wani mutum ya ce: “Wallahi lallai wannan rabo ba a yi adalci ba cikinsa, kuma ba a yi nufin fuskar Allah da shi ba.” Sai na ce, “Wallahi zan bai wa Annabi (SAW) labari, na tafi gare shi na ba shi labari.” Sai ya ce: “Wane ne zai yi adalci idan Allah da ManzonSa ba su yi adalci ba? Allah Ya jikan Musa (AS) an cutar da shi fiye da wannan amma ya yi hakuri.”