Daily Trust Aminiya - BUHARI DA MUSLIM
Subscribe

BUHARI DA MUSLIM

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Talatin da Shida: Yadda ake zartar da alkawarin kafiran amana. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ko dai ka ji tsoron wani ha’inci daga wadansu jama’a ka zartar musu da alkawari bisa daidai….”(K:8:58).

121. An karbo daga Abul Yaman ya ce: “Shu’aib ya ba mu labari daga Zuhuri ya ce, Humaid dan Abdurrahman ya ba mu labari cewa: “Lallai Abu Huraira (RA) ya ce: “Abubakar ya sanya cikin wadanda ya aika domin su sanar a Ranar Layya a Mina cewa: Wani mushiriki ba zai sake Hajji ba bayan wannan shekara, kuma babu wanda zai sake Dawafi a tube (tsirara). Kuma Ranar Hajji Babba ita ce Ranar Layya, saboda fadar mutanen cewa: Akwai Karamin Hajji a ran nan Abubakar ya zartar da alkawarin kafiran amana a wannan shekara. Saboda haka babu wani mushiriki wanda ya yi Hajji a Hajjin Ban-Kwana lokacin da Annabi (SAW) ya yi Hajjin Ban-Kwana.”

Babi na Talatin da Bakwai: Laifin wanda ya yi alkawari kuma ya yi yaudara. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Wadannan da suka yi alkawari, sa’an nan suka warware alkawarinsu cikin kowace shekara alhali su ba su takawa….” (K:8:56).

122. An karbo daga Kutaiba dan Sa’id ya ce: “Jarir ya ba mu labari daga A’amashi daga Abdullahi dan Murratu daga Masruk daga Abdullahi dan Amru (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Abubuwa hudu wanda duk ya kasance cikinsu ya kasance tsantsan munafiki. Wanda idan ya yi magana zai yi karya. Idan ya yi wa’adi zai saba. Idan ya yi alkawari zai yi yaudara. Idan ya yi fada sai ya fajirce (ya rika fadin bakar magana ga abokin fadarsa saboda kada su shirya). Kuma duk wanda ke da daya daga cikin wadannan siffofi to yana da daya daga cikin siffofin munafinci har sai ya bar ta.”

123. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Safiyan ya ba mu labari daga A’amashi daga Ibrahim Taimiyyu daga babansa daga Aliyu (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Ba mu rubuta komai daga Annabi (SAW) face Alkur’an da abin da  ke cikin takardar nan. Annabi (SAW) ya ce: Garin Madina harami ce tun daga A’ir zuwa wuri kaza. Wanda duk ya farar da wani abu, ko ya taimaka ga dan bidi’ah to la’anar Allah tana kansa da ta mala’iku da mutane gaba daya. Ba za a karbar masa dukkan wani aiki ba, kuma alkawarin Musulmi daya ne mutum guda na tafiya da shi ga wadanda ba su nan. Wanda ya wulakanta wani Musulmi la’anar Allah tana kansa da ta mala’iku da mutane gaba daya. Ba za a karba masa dukkan wani aiki ba. Haka kuma wanda ya shugabanci wani al’amarin Musulmi ba tare da izinin shugabancinsu ba, to la’anar Allah tana kansa da ta mala’iku da mutane gaba daya. Ba za a karba masa dukkan wani aiki ba.”

Kuma an karbo daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Yaya halinku zai kasance idan ya zamo ba ku samun Dinari da Dirhami daga kafiran amana? Sai aka ce masa: “Yaushe kake tsammanin faruwar wannan ya Abu Huraira? Ya ce: “Eh, ina rantsuwa da wanda ran Abu Huraira ke hannunSa na fahimci haka ne daga fadar mai gaskiya abin gaskatawa (Annabi SAW). Sai suka ce, “Kamar yaya? Ya ce: ‘Za a rika tozarta amanar Allah da amanar Manzon Allah (SAW), sai Allah Ya kuntata bisa ga zukatan kafiran amana sai su hana abin da ke hannayensu (jiziya).”

Babi na Talatin da Takwas: Kamar yanda ya gabata:

124. An karbo daga Abdan ya ce: “Abu Hamza ya ba mu labari ya ce, na ji daga A’mashi ya ce: “Na tambayi Abu Wa’il shin ko ka halarci Yakin Siffin? Ya ce, “Na’am. Sai na ji Sahlu dan Hunaif yana cewa: “Ku zargi bin son ranku, saboda lallai na gan ni a ranar da Abu Jandal (ya zo cikin sarka, amma Annabi (SAW) ya mayar da shi zuwa ga wadanda ya kulla sulhu da su a Ranar Hudaibiyya), saboda haka ran nan da ina da ikon canja umurnin Annabi (SAW) da na musanya shi. Kuma ran nan ba mu aje takubbanmu bisa kafadunmu ba. Saboda abin da ke firgita mu, har sai da (Allah) Ya musanya mana zuwa ga al’amarin da muka fahimci shi ya fi abin da muke kai (na niyyar yakar abokan gaba).”

texem
More Stories