✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi   297. An karbo daga Ubaidullahi dan Musa ko ya ce: “Dan Salam ya ce, Dan Juraij ya…

Tare da Sheikh Yunus Is’hak

Almashgool, Bauchi

 

297. An karbo daga Ubaidullahi dan Musa ko ya ce: “Dan Salam ya ce, Dan Juraij ya ba mu labari daga Abdulhamid dan Jubair daga Sa’id dan Musayyab daga Ummu Sharik (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya umarci da a kashe tsaka, saboda ta kasance tana hura wuta ga Ibrahim (AS).” (Tarihi ya nuna cewa lokacin da aka jefa Ibrahim (AS) a cikin wuta dukkan dabbobi sun yi kokarin kashe wutar face tsaka ita ce take hurawa).

298. An karbo daga Umar dan Hafsu dan Ghiyas ya ce: “Babana ya ba mu labari ya ce, A’amashi ya ba mu labari ya ce Ibrahim ya ba mu labari daga Alkamatu daga Abdullahi (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “Lokacin da wannan aya ta sauka cewa: “Wadannan da suka yi imani kuma ba su cadanya imaninsu da wani zalunci ba…” (K:6:83). Sai muka ce: Ya Manzon Allah! Wane ne cikinmu bai zalunci kansa ba? Ya ce, “A’a, ba yadda kuke nufi ba ne, abin nufi wanda ya cudanya imaninsa da shirka (hada Allah da wani). Shin ba ku ji maganar Lukman ga dansa ba ne cewa: “Ya Dan dana! Kada hada Allah da wani, lallai hada Allah da wani zalunci ne mai girma…” (K:31:13).

299. An karbo daga Is’hak dan Ibrahim ya ce: “Nasar ya ba mu labari ya ce, Abu Usamatu ya ba mu labari daga Habban daga Abu Zur’ah daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce: “An taba zuwa ga Annabi (SAW) da wani nama. Sai ya ce: “Allah zai tara mutanen farko da na karshe a wuri daya, sai ya jiyar da su da wani mai kira ya fitar da idanuwarsu ya kusantar musu da rana, sai ya ambaci Hadisin ceto. Sai su tafi ga Ibrahim (AS) sai suna cewa: “Kai Annabin Allah ne kuma masoyinSa cikin duniya ka neman mana ceton Ubangijinka. Sai ya ambaci karairayinsa (maganar da ya yi bisa nufin tabbatar da gaskiya). Sa ya ce: “Ta kaina nake! Ta kaina nake! Ku tafi zuwa ga Musa (AS).”

300. An karbo daga Ahmad dan Sa’id ya ce: “Abu Abdullah ya ba mu labari ya ce, Wahad dan Jarir ya ba mu labari daga babansa daga Ayyub daga Abdullahi dan Sa’id dan Jubair daga babansa daga Dan Abbas (Allah Ya yarda da su), daga Annabi (SAW) ya ce: “Allah Ya jikan mahaifiyar Isma’il (AS) ba domin ta yi gaggawa ba da ruwan Zam-Zam ya kasance babban kogi mai gudana cikin duniya.” Usman dan Abu Sulaiman yana zaune tare da Sa’id dan Jubair sai ya ce ba haka Dan Abbas ya ba ni labari ba, amma dai shi ya ce: “Ibrahim da Isma’il (AS) sun zo da mahaifiyarsa (Isma’il) lokacin da take shayar da shi kuma dauke da salkar fata tare da ita.”

301. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Abdurarrazak ya ba mu labari ya ce, Ma’amar ya ba mu labari daga Ayyub Sikhtiyan da Kasir dan Kasir dan Mudallib dan Abu Wada’ah daya na kari bisa ga maganar da nuwa. Sun karbo daga Sa’id dan Jubair ya ce, “Dan Abbas ya ce: “Mace ta farko da fara daura damara ita ce mahaifiyar Isma’il (AS) saboda ta boye gurabanta (lawalinta) daga kishiyinta Saratu. (Ibrahim ya auri Hajara don haka a lokacin da ta samu cikin Isma’il ta haife shi sai kishi ya kama Saratu). Sa’an nan Ibrahim ya tafi da ita da danta Isma’il lokacin da take shayar da shi har sai da ya sanya su (kai su) kusa da Dakin Ka’aba a karkashin wata itaciya inda Zam-Zam take a Madaukakin Masallaci lokacin babu kowa a Makka. Kuma babu ruwa tare da ita don haka ya sanya su a wannan wuri. Kuma ya sanya babban buhu cike da dabino da salkar ruwa (wurin tara ruwa). Sa’an nan Ibrahim (AS) ya juya zai tafi, sai mahaifiyar Isma’il (AS) ta ce, “Ya Ibrahim! Ina za ka tafi ka kyale mu a wannan kwari babu mutum, kuma babu komai? Sai ta rika fada masa haka tana maimaitawa yana tafiya bai ko waiwaya ba zuwa gare ta, sai ta ce: “Shin Allah ne, Ya umarce ka da wannan? Ya ce, “Na’am.” Ta ce: “To! Allah ba zai tozarta mu ba.”