✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ga INEC: Ku yi zabe na gaskiya da adalci a 2003

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta tabbatar da yin adalci a zabuubukan da za a yi a watan Janairu…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta tabbatar da yin adalci a zabuubukan da za a yi a watan Janairu da na nan gaba.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawa da Shugaban Hukumar INCE, Farfesa Mahmoud Yakubu da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, wadanda suka je domin yi masa karin bayani dangane da yadda zabubbukan bara suka kasance da shirin da aka yi na karasa wasu da ba a kammala ba a watan Janairun nan.

A sanarwar da Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina ya fitar, Shugaba Buhari ya bukaci Hukumar INEC ta tsaya kai-da- fata wajen yin adalci da bin doka a dukkan zabubbukan da za ta gudanar, ta yadda ’yan Najeriya da duniya za su yi amanna da ingancin zabubukan. “Dole ne kowane dan Najeriya ya samu damar zabar wanda yake so ba tare da fuskantar wani kalubale ba,” inji Shugaba Buhari. Wannan matsayi na Shugaban Kasar yana zuwa ne bayan kammala zabbubukan gwamnonin jihohin Kogi da Bayelsa da kungiyoyin masu sanya ido na ciki da wajen Najeriya suka ce an tafka magudi da keta doka.

’Yan adawa sun ce ba abin da zai sauya a zabubbukan cike gibin da za a gudanar, inda Injiniya Buba Galadima daya daga cikin manyan masu hamayya da gwamnatin APC ya shaida wa BBC cewa  “Shugaban ya sha fadar za a yi zaben adalci amma abin da ya faru a Kogi da Bayelsa ya nuna ba abin da zai sauya.”Sai dai a nata bangare Hukumar INEC ta ce tana bakin kokarinta wajen tabbatar da ganin ana samun ci gaba a zabubbukan kasar nan.

A wani labarin kuma Kotun Koli ta tabbatar da zaben Gwamna Sani Bello na Jihar Neja

Kotun Koli ta yi watsi da karar da dan takarar Jam’iyyar PDP, Umar Nasko ya shigar gabanta inda ya kalubalanci nasarar Abubakar Sani Bello a zaben Gwamnan.

Kotun ta tabbatar da sahihancin zaben da aka yi da kuma gaskata hukuncin da Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta yi a baya kan zaben.

A wani labarin Jagoran Jam’iyyar APC ta Kasa Cif Bola Tinubu ya kai wa Shugaba Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja. Shugaba Buhari ya tattauna da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a asirce.

Mai ba da shawara ga Shugaba Buhari kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa mutanen biyu sun tattauna a ranar Talata a fadar Shugaban Kasar da ke Abuja.

Tinubu dai ya taka muhimmiyar rawa a zaben Shugaba Buhari a zaben 2015 da 2019.