Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Buhari ga Osinbajo: Ina gudun kada cincirindon jama`a su tumurmushe ka

Buhari ga Osinbajo: Ina gudun kada cincirindon jama`a su tumurmushe ka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ja hankalin mataimakinsa Yemi Osinbajo akan ya yi kaffa-kaffa da shiga cikin turmutsutsun `yan kasuwa da suke cincirindo a kasuwannin da yake ziyara don ci gaba da kaddamar da shirin nan na gwamnatin tarayya na tallafawa mata masu kananan sana`o`i da karamin bashi wanda ake aiwatarwa a karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa.

Da yake bayani a liyafar buda baki da aka shirya a fadar shugaban kasa a jiya Litinin shugaba Buhari cewa, ya yi “Akan wannan shiri na kuxin kasuwa ina gargadin ka da ka yi taka-tsantsan wajen shiga cikin turmutsutsun jama` a kasuwannin da ka ke ziyara don gudun ka da su tumurmushe ka ganin yadda na ga mata masu kiba suna tunkararka a cikin kasuwannin.”

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa, duk da cewa shirin na baiwa kananan `yan kasuwa rancen kudin da suka kama daga Naira dubu 5 zuwa dubu 10 ya samu gagarumar nasara wajen tallafawa kananan `yan kasuwa musamman ma mata wajen inganta sana`ar su da kuma rayuwarsu.