✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ka tallafa wa ’yan kasuwar Arewa maso Gabas – Guragusku

Wani jigo a Jam’iyar APC kuma fitaccen manomi a Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Guragusku, ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taimaka wa…

Wani jigo a Jam’iyar APC kuma fitaccen manomi a Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Guragusku, ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taimaka wa ’yan kasuwar Jihar Yobe kan matsalolin da suka tsinci kansu a ciki, sakamakon rikicin Boko Haram da ya addabi yankin a tsawon shekara 10.

Alhaji Ibrahim ya yi kiran ne lokacin da yake zantawa da Aminiya ta tarho, inda ya ce akwai bukatar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mayar da hankali wurin taimaka wa ’yan kasuwar yankin Arewa maso Gabas, ta hanyar amfani da asusun Gwamnatin Tarayya wurin saye amfanin gonar da suke nomawa, domin sanya shi a rumbun ajiya na gwamnati don raba su ga ’yan gudun hijira ko wadanda bala’in guguwa da ruwa da iska ko gobara suka shafa. “Kun ga idan aka samu wannan zai zama gwamnati ta riski riba guda biyu, ga tallafa wa manoma ga kuma agaza wa rayuwar wadanda suke bukatar tallafi daga gwamnati. Don haka ya dace Shugaba Buhari ya dukufa wajen sayen amfanin gona a hannun manoman  Arewa maso Gabas don suna matukar bukatar haka,” inji shi.

Alhaji Ibrahim ya yaba wa Shugaba Buhari bisa kokarin da yake yi don bunkasa harkokin noma a kasar nan tare da bullo da shirin noman shinkafa a jihohin Kaduna, Kano, Jigawa da Katsina, domin samar da wadatacciyar shinkafa a kasar nan, wanda a cewarsa hakan zai farfado da tattalin arzikin kasa tare kuma da dogaro da kai a fannin abinci.

Da yake tsokaci game da kokarin Gwamnatin Tarayya  na hako man jetur a jihohin Bauchi da Borno, ya ce wannan yunkurin ba karamin ci gaba ba ne wanda yankunan za su samu tare da samar wa matasa aikin yi a jihohin, yana mai  cewa hakan zai rage zaman banza a tsakanin matasan Najeriya.

Ibrahim ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari, bisa ga irin kakarin da ya yi wurin samar da zaman lafiya a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, ta fuskar murkushe Boko Haram ta hanyar amfani da karfin sojoji masu kwazo wurin yaki.

Ya ce yanzu yankin Arewa maso Gabas, “Sai dai mu ce masha Allah tare da nuna goyon bayanmu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni da sauran gwamnonin Arewa maso Gabas bisa kokarin da suke yi na farfado da yankin da dawo da Najeriya cikin hayyacinta,” inji shi.

Ya shawarci al’ummar Jihar Yobe su ci gaba da ba da goyon bayansu ga Shugaba Buhari kan kokarin yake yi na sake farfadowa da gina yankin Arewa maso Gabas bayan ta’adin da mayakan Boko Haram suka yi wa yankin.

“Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya cancanci mu yaba masa kan tsare-tsare da shirye-shiryen da ya zo da su na samar wa matasanmu ayyukan yi da  kokarinsa na taimakawa ta fuskar noma. Sannan ga taimakon da ya kawo ga yara dalibai ’yan asalin jihar da suke karatu a kasashen waje ga kuma yunkurinsa na farfado da kamfanonin da suke jihar da suka durkushe, wadannan ayyukan abin a jinjina wa Gamna Mai Mala Buli ne,” inji manomin.

Ibrahim ya yi kira ga gwamnatin Jihar Yobe ta yi kokarin hada karfi da karfe da manoman jihar domin bunkasa noma da tattalin arzikin jihar. Ya ce, muddin gwamnatin jihar ta shiga cikin lamarin za a samu bunkasar tattalin arziki ta fuskoki daban-daban, sai ya nemi Gwamnan Jihar ya rika sayen kayan gona da manoman jihar suka noma domin karfafa musu gwiwa.

Daga karshe ya gode wa Shugaban Kasa da jami’an tsoro kan kokarinsu wajen samar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas inda a sakamakon haka ya janyo hankalin Fulani makiyaya daga kashashen Nijar da Kamaru da Chadi suke shigowa yankin domin yin kiwonsu ba tare da fuskantar wata fargaba ba.