Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Buhari: Kafin zaben 2019! (1)

Buhari: Kafin zaben 2019! (1)

Wannan bayani ko zance da nake so in soma daga yau, ina so ne ya kasance tamkar manuniya da za mu iya amfani da ita game da zaben 2019 da za a yi nan da watan Fabrairu mai zuwa. Wato mu yi waiwayen baya domin gano yadda tafiyar ta kasance daga shekarar 2015 zuwa yau, sa’annan mu yi kokarin ganin ko alkaluma sun yi daidaito game da zaben da za mu yi, ko kuma an samu riba ko faduwa daga noman da muka yi a kakar zaben da ta wuce.

Kafin in kawo wadannan nasarori ko faduwa da aka yi, bari mu dan yi waiwaye tukuna. Idan an lura da kyau, daga abin da ya faru a zaben 2015 da nasarar da Jam’iyyar APC ta samu an fahimci babban dalilin da ya sa aka samu nasara, ba kuma komai ba ne face ’yan Najeriya sun gano bakin zaren, ba abin ya dace su yi a daidai wancan lokaci sai su yi wancakali da Jam’iyyar PDP.. Ba kuma wani abu ya jawo wannan turjiya da al’ummar Najeriya suka yi ba sai ganin cewa Jam’iyyar PDP ta kasance mai wahalar da mutane! Jam’iyyar PDP ta sa al’umma cikin bala’i da ukuba! Jam’iyyar PDP a daidai lokacin ba abin da ta iya sai samar da rashin wutar lantarki da ruwan sha da rashin aikin yi! Yawancin mutanen kasar nan sun aminta cewa Jam’iyyar  PDP a daidai wancan lokaci ba abin da ta iya face bakin mulki! Haka kuma an yi tarayya cewa Jam’iyyar PDP ta gina talauci da rashin ingantaccen kiwon lafiya a tsakanin jama’ar kasar nan ne!

Idan mun tuna a daidai wancan lokaci ba irin abin da talakawa ba su fada ba game da irin mulkin Jam’iyyar PDP. Wadansu daga sashin talakawa na ganin cewa ta yaya za a yi a zabi irin wannan jam’iyya ta PDP da ta yi shekaru tana sa talaka cikin kunci da wahala. Saboda haka, tun da talauci da wahala da kunci bai san bambancin addini ba, talakawan Najeriya suka hadu suka canja wancan gwamnati, yanzu sai labari.

Sai dai ni ko a lokacin da ake ta wancan kokari na kawar da Jam’iyyar PDP, ina da tababa na ganin cewa da an kawar da Jam’iyyar PDP shi ke nan matsalolin Najeriya sun kau. Na samu wannan shakku ne saboda sanin irin halayyar mutanen kasar nan na kasancewa matsalar kasar, ba Jam’iyyar PDP ba. A cikin kundun zuciyata abubuwa da dama ke rayawa tun wancan lokaci. Yawancinmu, wadanda suka yi ta yekuwa da fafutikar sai an kawo canjin, imaninmu ragagge ne. Haka kuma amanna da alwashin da ke tattare da yawancinmu game da canjin, ragaggu ne. Kamar yadda na sha taunawa, ire-iren wadannan mutane da muke da su, su ne matsalarmu ba Jam’iyyar PDP ba.

A lura da abin da na jaddada, matsalar tamu ce ba ta jam’iyya ba. Koda aka kawar da Jam’iyyar PDP, APC ta hau, Baba Buhari ya zama dakare kuma har yanzu abubuwa ba su gyaru ba irin yadda ake so, ni ban yi mamaki ba. Lallai an kokarta wajen cin dunun Boko Haram, an kuma sa takunkumi mai kauri na hana sata da almundahana, amma ba mai cewa an ga karshen wadannan lamura, duk da cewa an kawar da Jonathan da Jam’iyyar PDP. Ba kuma wai ina nufin dole a ga komai ya yi tsaf ne da hawan Jam’iyyar APC da Shugaba Buhari ba, domin kuwa barnar shekara 16 ba ta gyaruwa cikin shekara 3 ko 4. Ko alama! Inda Gizo ke sakar shi ne ko mu ’yan Najeriyar da muka rayu da gwamnatin Jonathan da Jam’iyyar PDP mun canja, mun kuma hau turbar gyara da Jam’iyyar APC ta shimfida, Shugaba Buhari ke yi wa jagoranci? Shin allurar canji ta shige mu kuwa, ko kuwa dai mun zura ido ne abubuwa su canja saboda Shugaba Buhari ya hau mulki,saboda shi ne allan-musuru. Idan an ga rana ta kunno daga gabas sai mu cicciba domin kawo canjin da muke bukata? Shin har yanzu gwamnatin Jonathan ce ke mulki da har kullum abubuwa suka ki motsawa sai mu ce ita ce matsala? Shin ko Shugaba Buharin ba shi ke mulkin ba ne, wani ne can daban? Me ya sa ba za mu canja ba tunda Shugaba Buhari ya ci zabe, yana ta mulki ba Jam’iyyar PDP ba?

Tabbas  har yanzu gwamnatin APC ce ke mulki, kuma manufofin da aka kafa gwamnatin bisa kansu, suna nan har yanzu. Amanna da gwamnatin kuma ba ta kau ba, domin zabarta aka yi, an kuma san ta gaskiya ce. Haka kuma shi Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo ya aminta da Buhari da tsarinsa. Da shi aka assasa gwamnatin; kuma manufofinta yake bi domin aiwatarwa. Haka ministoci da wadansu daga cikin gwamnoni duk na Baba Buhari ne, amma me ya sa ake ta kokawa? Kila inda gizo ke sakar shi ne yadda mutanen Najeriya suka kasa ko suka ki canjawa a cikin tsawon shekarun da Buhari ke mulki. Wannan shi ne ya kara tabbatar da cewa Buhari ne son canji da neman kawo canji, sauran mu ’yan Najeriya, muna nan muna jira Shugaba Buharin ya yi nasa siddabarun da canji zai samu, sa’annan mu kuma za mu canja halaye ko kyautata al’amuran da ke dakile kasar nan. Wannan ne ya sa na kara tabbatar da zancen da na sha yi na cewa, akwai masoya Buhari da kuma masoyan Buhari. Wani na iya cewa ai ba wani bambanci tsakanin wadannan al’umma biyu!

Akwai bambancin tsakanin irin wadannan mutane. A halin da muke ciki duk wanda ka ji yana ta tunanin ai canji ya kusa dauwama, tunda Buhari ya kasance Shugaban Kasa,saboda haka a kara hakuri, sauran kiris a kai karshen wahalhalun da ke addabar kasar nan, to MASOYIN Buhari ne, amma ba masoyin kawo canji ba. Irin su ne ke biye da akida da ruhi da tunani na irin gwamnatin Buhari da irin aljannar da talaka zai shiga a lokacin da Buhari ya sake hayewa kan karagar mulki a 2019. Ma’ana, irin wadannan mutane ba sa ganin komai sai ci gaban da Buhari zai kawo wa Najeriya in ya sake hawa karo na biyu, ba tare da dubi zuwa ga irin tasu gudunmawar wajen kawo wa Najeriya canjin ba!

Irin wadannan mutane suna tare da Buhari a kowane irin fasali, amma sun bambanta da MASOYA Buhari. Ta yaya? Wadanda suke MASOYA Buhari, ba irin wadancan gungun da muka yi bayani a baya ba ne! Su MASOYA Buhari, su ne wadanda ke biye da akidojin Buhari da tunanin Buhari da tausayin Buhari da gaskiyar Buhari da kuma kima da daukaka ta Buhari! Akwai su kuma da dama a cikin kasar nan, wadansu ba ma ’yan siyasar ba ne. Wadansu ba kuma ’yan Jam’iyyar APC ba ne! Suna nan jibge! Irin wadannan MASOYA na Buhari ba su kallon Buhari a matsayin ma’asumi. Ba sa tsauwala wa jama’a idan sun kasance masu sayar da tumatir ko doya ko dankali ko shinkafa ko man gyada ko kuma in sun haye kan doron mulki! Irin wadannan MASOYA na Buhari za ka gan su cikin kamala da da’a, ba wai haka nan sakayau ba, kamar dabbobi! MASOYA Buhari ba sa neman kazamar riba! Ba sa cin mutuncin ’yan uwa. Ba sa cin hanci da yin bocar iska a duk inda suke aikin gwamnati! Ba sa kuma yin algushu, idan an ba su kwangila! Ba sa gudun ganganci da kabu-kabu ko wani abin hawa, suna kashe da gurgunta mutane a bisa titi! Ba sa ajiye mota ba bisa ka’ida ba! Ba sa zunde da gulma da zagin mutane! Ba sa yin dukan wani abu da ba bisa ka’ida yake ba! Kai in gajarce maka, MASOYA Buhari ba sa nuna rashin da’a a koyaushe! MASOYA Buhari masu gaskiya da rikon amana ne, ko Buhari na nan ko ba ya nan! Ko Buhari zai sake cin zabe ko zai fadi, domin ba bautar Buhari suke ba, kasarsu suke yi wa hidima!

Za mu ci gaba