✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

BUHARI KARO NA BIYU: Muhimman batutuwan da ya kamata ya fuskanta

Masu fashin baki, ’yan siyasa da sauran ’yan Najeriya da dama sun yi tsokaci kan abubuwan da suke gani ya dace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari…

Masu fashin baki, ’yan siyasa da sauran ’yan Najeriya da dama sun yi tsokaci kan abubuwan da suke gani ya dace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya maida hankali a kansu, musamman ganin cewa zai hau karagar mulki a zagaye na biyu nan da kwanaki biyar masu zuwa.

Shugaba Buhari, wanda ya lashe zabe a zagaye na biyu  a watan Faburairun bana za’a rantsar da shi tare da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a ranar Laraba mai zuwa.

Shi dai shugaban, wanda ya dare mulki a zagaye na farko a ranar 29 ga watan Mayun 2015, ya yi alkawura da dama ga al’ummar Najeriya, musamman abubuwan da suka shafi magance rashin tsaro a yankin Arewa maso gabas, inda ’yan ta’addar kungiyar Boko Haram suka halaka dubunnan mutane kuma suka lalata garuruwa, makarantu, kasuwanni, asibitoci da wuraren ibada na Musulmi da Kirista. Sa’annan kuma ya yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa da kuma kokari wajen farfado da tattalin arzikin kasa.

Masu fashin baki sun bayyana cewa a cikin shekaru hudu da suka gabata, hakika Shugaba Buhari ya yi iyakacin kokarinsa kuma ya samu yabo a wasu wurare amma kuma akwai mutane da dama da ke ganin cewar kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, ganin yadda tattalin arziki ya kara sukurkucewa, sha’anin tsaro ya tarwatse a wasu yankuna na kasar nan, sa’annan kuma hadin kai tsakanin jama’ar yanki daban-daban na kasar nan ya lalace.

Tuni dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP da dan takarar Shugaban Kasarta, Atiku Abubukar suka garzaya kotu domin kalubalantar zaben Shugaba Buhari. Sai dai a bisa tsarin mulkin Najeriya, hakan ba zai hana a rantsar da shi ba.

Bayan kammala zabe ne shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus da kuma Atiku Abubakar suka zargi Shugaba Buhari da rashin iya tafiyar da mulki da nuna bambanci da kuma nuna halin ko-oho kan halin da ’yan Najeriya sama da miliyan 200 suke ciki.

Amma kuma Ministan Watsa Labarai Alhaji Lai Mohammed da Shugaban Sojojin Najeriya Janar Buratai, sun yi zargin cewa ’yan adawa na kokarin lalata mulkin Shugaba Buhari ta hanyar yi masa zagon kasa da kuma daure gindi ga ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

Abubuwa da dama sun faru, wasu sun faranta wa ’yan Najeriya rai, wasu kuma sun sosa musu ziciya, ganin cewa ana ganin shi Shugaba Buhari, wanda gogaggen soja ne da ya taba hayewa karagar mulki shekaru talatin da suka gabata, kafin ya sake dawowa a karkashin farar hula; ya dace a ce ya yi rawar gani fiye da abin da ake gani a halin yanzu.

Mutane da dama sun bayyana rashin jin dadinsu kan cece-kucen da ke faruwa tsakanin ’yan adawa da gwamnati kuma sun yi kira ga Shugaba Buhari da ya maida hankali wajen aiki ga jama’a a sabuwar damar da ya samu.

Da yake bayani kan abubuwan da yake so Shugaba Buhari ya maida hankali, wani Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Barno, Mohammed Tahir Monguno, cewa ya yi kamata ya yi Shugaba Buhari ya ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa da ya fara a karon farko. Ya kara da cewa ya kamata Shugaba Buhari ya kara kaimi game da batun noma.

“Ina ganin zai dace idan a karo na biyu Shugaba Buhari ya mayar da hankali sosai a kan yaki da cin hanci da rashawa domin kuwa wannan abu ne da yai wa kasar nan ta’adi sosai,” inji shi.

“Kamar yadda kowa ya sani ne, a wannan karon na farko Shugaba Buhari ya yi iya kokarinsa na ganin cewa an yi yaki da cin hanci da rashawa. Zai dace a ce an ci gaba da hakan.

“Sai batun aikin noma, wanda idan an kara mayar da hankali zai bunkasa ayyuka a kasar nan sosai. Hakan zai bunkasa tattalin arzinkin kasar nan sosai kuma matasa za su samu aikin yi.

“Wani muhimmin abu kuma shi ne batun tsaro. Mun ga gwamnati ta magance Boko Haram matuka amma sai ga wasu fuskokin rashin tsaro kamar garkuwa da mutane sun taso.

“Ina ganin zai dace gwamnati ta mayar da hankali kan harkar tsaro sosai. Ka ga idan an magance rashin tsaro, mutane za su iya zuwa gonakinsu ba tare da fargaba ba,” a cewar Monguno.

Wani Dan Majalisar Tarayya, wanda bai so a bayyana sunansa, ya ce Shugaba Buhari ya dace ya matsa kaimi domin ganin cewa ya gyara tattalin arzinkin Najeriya domin ci gaban kasa.

Shi ma dai ya kalubalanci shugaban da ya yi amfani da kujerarsa don ganin cewa ya magance matsalar rashin tsaro a kasa.

Har ila yau, wani wanda shi ma bai so a bayyana sunansa, ya ce idan har Shugaba Buhari na bukatar ya samu nasara a mulkinsa karo na biyu, dole ne ya yi waje da wasu daga cikin minitocinsa da wasu masu yi masa hidima, domin kuwa ba abin da suka kara masa a mulkinsa sai bakin jini.

Yana mai cewa kasa kamar Najeriya tana bukatar mutane masu kishi, ba kawai mutanen da sun sa son rai a gaba ba.

Shi kuma Alhaji Bashir Musan Sati, Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Filato, cewa ya yi Shugaba Buhari ya samu nasarori a karon farko na wa’adin mulkinsa, duk da cewa ya hadu da kuraye a cikin fatar raguna amma duk da haka Allah Ya sa ya cin ma biyan bukata.

“Nasarorin da Buhari ya cin mawa a wa’adinsa na farko sun hada da yadda ya magance fitinar Boko Haram, sannan ya magance sata domin a yanzu an bude kofar baitulmalin kasa ga mutane sun shiga ciki amma suna tsoron yin sata” inji Musan Sati.

“Bayan haka, wadanda suka yi sata duk abin da suka tara a yanzu ana kwatowa kuma ana yi wa talakawa aiki, sannan Buhari ya shimfida ayyuka da suka hada da tashar jirgin ruwa ta Baro a Jihar Neja, ita kadai ta isa ta ba mutum mamaki.

“Sannan darajar Buhari ta sa girman Najeriya da daukakarta sun karu a kasashen duniya, ga kuma hanyoyin jirgin kasa da na mota da ake kan shimfidawa,” inji shi.

Da aka tambaye shi ko a wane fanni yake ganin ya dace Shugaba Buhari ya mai da hankali a karo na biyu, Sakataren Jam’iyyar APC a Jihar Filato cewa ya yi: “Abu na farko, tun da ina cikin wannan gwamnati da za mu fi mayar da hankali a kansu a zango na biyu, ina so mu ci gaba da kare rayukan mutane da kuma dukiyoyinsu.

“Ya kamata Buhari ya kara sa kaimi don mutane su ci moriyar arzikin da ke kasarsu, wato a mayar da hankali ga bangaren noma da kuma hakar ma’adanai. Sannan akwai hanyoyinmu da yawa da suka lalace ba mu da shakka kuma ba ma shayi za a gyara wadannan hanyoyi, kamar yadda aka fara gyara hanyar Akwanga zuwa Abuja,” inji Musan Sati.

Dabou Mann, dan Jam’iyyar PDP kuma tsohon Kwamishinan Kudi ne a Jihar Filato. Cewa ya yi Shugaban Buhari ya yi kokari wajen yaki da matsalar tsaro a yankin Arewa maso gabas amma kuma yanzu matsalolin rikicin manoma da makiyaya da sacewa da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kuma yadda ’yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin Arewa maso yamma na kawo wa Gwamnatin Buhari tarnaki.

“Sannan Buhari bai yi kokari a bangaren tattalin arziki da lafiya da kuma samar da ayyukan yi ba, sannan rayuwa ta yi tsada, a lokaci guda tattalin arziki ya tarwatse,” inji shi.

“Don haka abin da nake so Buhari ya mayar da hankali a karo na biyu shi ne bangaren tsaro, sannan ya samar da ayyukan yi, domin idan ka duba, kowace shekara dubban dalibai ake yayewa a kasar nan kuma ba su da aikin yi; don haka rashin aikin yi gare su zai haifar da matsalar tsaro,” inji shi.

Tsohon Kwamishinan ya kara da cewa, “ya kamata Buhari ya sani cewa matsalar tsaro ta sa masu zuba hannun jari da ke kasashen wajen kin zuba jari a Najeriya, inda hakan ya sanya rashin aikin yi ke ci gaba da karuwa, domin babu wanda zai sa kudinsa a kasar da ake kashe-kashe. Don haka ya kamata ya mayar da hankali kan tsaro.

“Ya kamata Buhari kuma ya farfado da masana’antu irin masaku da na rini da sauransu, hakan zai kara magance matsalar tsaro domin za su samar da aikin yi. Ya kamata ya kuma mayar da hankali kan noma da kiwo da kuma kasuwanci, inda idan ya yi hakan ayyukan yi za su samu, tattalin arzikin kasa zai bunkasa kuma aikata miyagun laifuka zai ragu. Sannan akwai bukatar ya mayar da hankali kan ilimi da bangaren Kimiyya da Fasaha,” inji shi.

Bello Lukman, fitaccen dan jarida kuma mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum, ya ce abu na farko da Buhari zai fi mayar da hankali shi ne, tsaro, saboda idan ka duba Buhari ya yi abubuwa masu yawa amma rashin tsaro ya dagula wa gwamnatinsa lissafi.

“Yanzu matsalar ’yan bindiga a Zamfara da Katsina da Sakkwato da kuma masu sace mutane don neman kudin fansa a hanyar Abuja zuwa Kaduna na ci gaba da bata Gwamnatin Buhari,” inji Lukman.

Ya kara da cewa, “ya kamata ya mayar da hankali a bangaren lafiya, a samar da asibitoci a kauyuka, a samar da inshorar lafiya ga ’yan Najeriya kamar yadda wadansu kasashe suke yi wa ’yan kasarsu, sannan gwamnati ta dauki nauyin likitoci ta tura kauyuka don kula da lafiyarsu.”

Barista Aminu Ibrahim, wani lauya mai zaman kansa, ya harzuka matuka ganin irin yadda Shugaba Buhari ya yabi ministocinsa a zaman ban kwana da ya yi da su a fadarsa da ke Birnin Tarayya Abuja a ranar Laraba da ta gaba ta.

“A gaskiya raina ya baci, ban yi tsammanin cewa Shugaba Buhari zai yabi ministocinsa ba, ganin cewar da yawa daga cikinsu ba su tabuka komai ba.

“Kuma hakika jikina ya yi sanyi, domin bisa ga dukkan alamu ba zai canza wasu da yawa daga cikinsu ba, ganin yadda yake ta yabonsu a lokacin da yake bankwana da su. Ina mai tabbatar maka da cewa akwai ’yan Najeriya da dama da ba su ji dadin wannan tsarin ba.

“To amma tunda tsarin mulki ya ba Shugaba Buhari dama ya yi aiki da irin mutanen da yake so, ni ina rokonsa da ya bayyan sabbin mininstocinsa a makon da aka rantsar da shi kuma ya fadada yawansu domin a dauki matasa masu hazaka da kuma mata a yi tafiyar da su. Fatanmu shi ne kada ya koma fadar Shugaban Kasa ya shagala kamar yadda ya yi a karo na farko, lokacin da sai da ya dauki watanni shida kafin ya nada ministoci,” inji Barista Ibrahim.

Wata mai suna Na’omi Jacob, wacce ke da shago a kasuwar Jabi da ke Abuja, cewa ta yi ya dace Shugaba Buhari ya rage fita kasashen waje domin ya tsaya ya yi wa mutane aiki.

“Ni kam na gaji da ganin yadda yake hawa jirgi yana yawo daga waccan kasa zuwa waccan kasa a lokacin da kasarsa ke fama da matsalolin rashin tsaro da lalataccen tattalin arziki,” inji Na’omi.

“Na tsorata matuka da na ji Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ya ce Najeriya za ta koma gidan jiya (recession). A lokacin da ya fada an yi ca a kansa, to amma ga shi Gwamnan Babban Banki, Godwin Emefele shi ma ya ce lallai akwai barazanar tabarbarewar arziki. Wannan alama ce da ke nuna cewar tilas Shugaba Buhari ya canza salon tsarin mulkinsa.

“Talakawa su ne suka zabe shi amma yanzu talakan Najeriya shi ya fi kowane talaka fama da talauci a fadin duniya. Wannan abin kunya ne ga Najeriya, wacce take daya daga masu arzikin man fetur a fadin duniya.

“Ni a ganina, kirarin da ake wa Shugaba Buhari cewa shi ba barawo ba ne bai isa ba. Ina amfanin badi ba rai? E, shi ba barawo ba ne amma akwai barayi da dama a karkashinsa kuma ya kasa hana su sata. Mu fatanmu shi ne ya samo mutane masu kwazo su taya shi aiki domin ci gaban kasa,” inji ta.

Da yake tofa yawu kan lamarin, wani babban malami a Jami’ar Abuja, Dokta Abubakar Umar Kari, ya bai wa Shugaba Buhari shawarar cewa ya canza dabarun da yake amfani da su wajen yaki da cin hanci da rashawa.

“Akwai dokokin kasa da dama da suka ba Shugaban Kasa damar amfani da karfin mulki domin gyara tafiyar da ake yi, don haka ina ganin ya dace ya yi amfani da wannan dama da Allah Ya ba shi a karo na biyu domin ya faranta wa ’yan Najeriya rai,” inji Dokta Kari.

Abin da jira a gani shi ne, ko Shugaba Buhari zai canja salon mulkinsa daga yadda ya gudanar a zangonsa na farko ko kuwa zai ci gaba daga inda ya dasa? Lokaci shi ne babban alkali.