Search
Subscribe
Buhari mai talakawa

Buhari mai talakawa

In ban da shugabannin da aka yi a Jamhuriyya ta Farko da ta Biyu kusan za a iya cewa ba a samu wani shugaba da talakawa suka nuna masa kauna na zahiri irin Shugaba Buhari ba. Hasali ma  idan mutum ya ce, irin kaunar da talakawa suka nuna wa Buhari ko shugabannin Jamhuriya ta Farko da ta Biyu ba su samu irinta ba, ba za a ce ya fadi ba daidai ba.

Domin saboda tsananin kaunar Buhari ne za ka ga talaka yana kwana da yunwa amma ba ya so ya ji an soki Buhari a gabansa, wanda ya sanya talakawa suka tabbatar da batun nan na Bahaushe da yake cewa ‘so hana ganin laifi,’ domin saboda tsananin kauna duk abin da Buhari ya aikata daidai ne a wurin talakawa magoya bayansa.

Akwai lokacin da wani mai motar haya ya dauki fasinja a cikin garin Abuja ana cikin hira sai ya ji daya daga cikin fasinjojin yana sukar Buhari, nan take ya taka birki ya ce masa ya sauka daga motarsa.

Haka kuma akwai wani mai sayar da dabino da wani ya kira shi ya sayi dabino na Naira 700, kafin ya biya sai aka kira shi ta waya, a cikin tattaunawar da suke yi sai mai dabinon ya ji wannan mutumin da ya sayi dabinon nan yana sukar Buhari ne,  nan da nan ya harzuka, da mutumin nan ya gama waya ya dauko kudin mai dabino Naira 700 ya ba shi sai mai dabinon nan ya ce ai dabinon ba na sayarwa ba ne. Ya kwace dabinonsa ya yi gaba, saboda tsananin kaunar Buhari ya gwammace ya koma gida bai yi ciniki ba da ya sayar da kayansa ga mai sukar Buhari.

Wadansu talakawan ma har kuka suke yi a duk lokacin da suka ga Buhari ido-da-ido saboda tsananin murnar sun gan shi a zahiri. Shi ya sanya duk inda ya je za ka ga talakawa sun yi fitar farin dango suna son ganinsa, idan da hali ma su gaisa da shi.

Shi ya sanya shi kansa Shugaba Buhari da limamai suka kai masa ziyara a makon jiya a karkashin jagorancin Farfesa Shehu Galadanci suka roke shi da ya rika zuwa Babban Masallacin Kasa na Abuja yana yin Sallar Juma’a maimaikon ya rika yi a masallacin fadar gwamnati, sai ya ce idan ya yi haka zai takura wa mutane da yawa, domin za a rufe duk hanyoyin da Shugaban Kasa zai bi ya je masallacin saboda dalilai na tsaro. Kuma akwai yiwuwar mutane su takura a masallacin saboda turereniya domin ganinsa ko son a gaisa da shi.

A farkon mulkinsa lokacin da ya yi Sallar Idi a Masallacin Idi na Abuja jami’an tsaro sun sha wahala bayan an tashi, domin mutane tasowa suka yi suna son gaisawa da Shugaba Buhari, da kyar aka samu ya shiga motarsa.

Talakawa suna tsananin kaunar Shugaba Buhari ne saboda sun yarda cewa shi ne zai iya fitar musu da kitse daga wuta, wato sun yarda zai iya magance mafi yawa daga matsalolin da suke damunsu wadanda suka shafi rayuwar yau da kullum.

Saboda haka ya kamata Shugaba Buhari ya tashi tsaye wajen ganin ya inganta rayuwar talakawan nan domin ya nuna godiyarsa da irin tsananin kauna da goyon bayan da suke nuna masa.

Akwai bukatar Shugaba Buhari ya himmantu wajen saukaka wa talaka radadin rayuwa ta hanyar samar da ayyukan yi da karfafa wa ’yan kasuwa da jari da taimaka wa manoma da duk abubuwan da za su saukaka musu yin noman tare da samar da hanyoyin sayar da amfanin gonar nasu. Matasa kuma a tabbatar sun samu ingantaccen ilimi, sannan kuma a fito da hanyoyin samun aiki gare su.

Babu shakka mutane sun ji jiki sosai kuma har yanzu suna jin jiki, talakawa sun daure sun sake zaben Shugaba Buhari a karo na biyu ne saboda sun amince cewa idan ya ci gaba da mulki za su kai ga biyan bukatarsu ta samun ingantacciyar rayuwa, saboda haka muna fata mataki na gaba da aka shiga ya zamanto mataki ne na buda-bakin azumin da talakawa suka yi a mataki na farko.

Lallai yakamata a dauki matakan saukaka wa talakawa halin kuncin rayuwar da suka shiga, ta haka ne za a samu raguwar aikata miyagun ayyuka, domin idan tsanani ya yi yawa yakan sanya mutumin kirki ya zama mutumin banza, saboda wahala za ta iya sanya shi ya aikata wani abu da bai dace ba.

Muna fata Allah Ya ba shugabanninmu ikon sauke nauyin da aka dora musu na inganta rayuwar talakawansu. Su dai talakawa sun yi nasu ta hanyar zaben shugabannin da suke ganin  za su yi masu aikin da ya dace, yanzu saura su kuma wadanda aka zaba su cika alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin