Search
Subscribe
Buhari na sauka APC ta gama yawo – Okorocha

Buhari na sauka APC ta gama yawo – Okorocha

Sanata Rochas Okorocha mai wakiltar Imo ta Yamma, ya dora laifin matsalar da ta dabaibaye Jam’iyyar APC a kan shugabanninta, ina ya ce in ba a yi hankali ba Buhari yana sauka daga mulki jam’iyyar za ta rushe.

Okorocha ya ce akwai alamomi ne da ke nuna cewa da wahalar gaske Jami’iyyar APC ta sake cin zabe a shekarar 2023.

Ya bayyana haka ne a Kano, lokacin da yake magana dangane da rikicin da ya kaure a tsakanin Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki da Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa Adams Oshiomhole.

Okorocha ya ce duk jam’iyyar da rigingimusuka dabaibaye ta, kuma shugabanninta suka kasa warware su, sai wasu rikice-rikice suke rurawa da kansu, to bai kamata a kira wannan jam’iyya ba, sai dai a kira ta jamhuru.

“Wadannan rigingimu da ke ta bijirowa cikin APC, suna nuna cewa jam’iyyar kara-zube kawai take. Babban kalubalenmu shi ne ba mu da wata alkibla ko manufa ko akida a jam’iyyarmu,” inji shi.

Ya ce idan ba hanzarta magance rigingimu da shugabannin APC ke haddasawa ba, to za a wayi gari a zaben 2023 an kwace mulki daga APC.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin