✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya aurar da diyarsa Hanan

Hanan ’yar autan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta zama amarya

An daura auren diyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Hanan da angonta Muhammad Turad Sha’aban.

Rahotanni sun ce an daura auren Hanan mai shekara 22 ne a Fadar Shugaban Kasa, a ranar Juma’a 4 ga watan Satumba, 2020.

Amaryar ita ce ’yar auta a cikin ’ya’yan Shugaba Buhari da mai dakinsa Hajiya Aisha.

Aisha Buhari da kanta ta wallafa hotunan amarya da angon a shafinta na Instagram a yammacin ranar Juma’a.

 

Rahotanni na cewa Fadar Shugaban na cike da farin ciki game da daurin auren.